AU ta dakatar da Madagascar bayan juyin mulki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar ƙasashen Afirka (AU) ta sanar da dakatar da Madagascar biyo bayan juyin mulki da sojojin ƙasar suka yi wanda ya hamɓarar da Shugaba Andry Rajoelina.

Shugaban AU, Mahamoud Ali Youssouf ya tabbatar da haka ga kafar labarai ta AFP a jiya Laraba, inda ya ce hukuncin zai fara aiki ne a nan take.

An ɗauki matakin ne bayan da wata tawagar manyan sojoji ta karɓe mulki jim-kaɗan da majalisar dokokin ƙasar ta tsige shugaban ƙasar.

Babbar Kotun Madagascar tuni ta tabbatar da Kanal Michael Randrianirina a matsayin sabon shugaba, lamarin da ya sauya akalar siyasa a ƙasar.

Hakan ya nuna yadda AU take tsayuwa wajen ɗaukar tsatstsauran mataki akan lamuran sauyin gwamnati a shiyyar.

By Babaji