Ƙungiyar NPAN ta bayyana damuwarta kan lafiyar Abdulgafar Alabelewe da Mista AbdulRaheem Aodu, wakilan Jaridun The Nation da Blueprint na Jihar Kaduna.
An sace su ne tare da iyalansu a Kaduna a daren ranar Asabar.
Wata sanarwa da shugaban NPAN, Malam Kabiru A. Yusuf ya sanya wa hannu, ta ce: “Abin da ya fi daukar hankali shi ne shiru da aka ji daga masu garkuwa da mutanen da suka kama ‘yan jaridan tare da iyalansu da suka hada da mata da yara.”
Malam Kabiru ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tura jami’an tsaro domin ganin an ceto dan jaridar da iyalansu daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.
“Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da an dawo da ‘yan jarida da iyalansu lafiya.
“Muna kira ga waɗanda suka yi garkuwa da su da su tabbatar da cewa babu ɗaya daga cikinsu da ya samu illa” in ji shi.
Hakazalika kungiyar NPC ta nuna rashin jin daɗin ta kan yadda aka yi garkuwa da wasu ‘yan jarida biyu mazauna Kaduna da iyalansu.
Da take mayar da martani kan lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, shugabar kula da hulɗa da jama’a, Chinyere Facah, ta ruwaito Sakatariyar Zartaswa, Dokta Dili Ezughah, tana cewa Majalisar ta kaɗu matuka game da sace Abdulgafar Alabelewe. wakilin jaridar The Nation; da Mista Abdulraheem Aodu na jaridar Blueprint, tare da matansu da ‘ya’yansu.
Ezughah ta ayyana waɗannan sace-sacen su ne na baya-bayan nan a jerin hare-haren da aka kai wa ‘yan jarida da kungiyoyin yada labarai a cikin shekara guda da ta gabata, daga bangaren gwamnati da masu zaman kansu.
Shugaban na NPC, ya yi kira ga jami’an tsaro su yi aiki don ganin an sako ‘yan jaridan da aka yi garkuwa da su da iyalansu ba tare da ɓata lokaci ba; sannan kuma a zaƙulo waɗanda suka aikata wannan aika-aika domin hukunta su.
