NRC ta buƙaci al’ummomin Abuja–Kaduna su taimaka wajen kare layin dogo

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC) ta yi kira ga al’ummomin da ke gefen layin dogo na Abuja zuwa Kaduna da su taka rawar gani wajen kare jiragen ƙasa da kayayyakin layin dogo, sakamakon ƙaruwar hare-hare da lalata kayayyaki da ake fuskanta a yankin.

Wannan kira na zuwa ne bayan karuwar ayyukan wasu bata-gari da ke kai hare-hare kan jiragen ƙasa tare da lalata sassan su, lamarin da hukumar NRC ta yi Allah-wadai da shi, tana mai cewa masu aikata laifukan sun samu damar aiwatar da ayyukansu cikin sauƙi a wasu wurare.

Hukumar ta bayyana cewa sabon harin da aka kai ya faru ne a kilomita 177 a kan layin Abuja zuwa Kaduna, inda wasu da ba a san ko su waye ba suka taru a bakin layin dogo suka rika jifan jirgin ƙasa da duwatsu yayin da yake tafiya, lamarin da ya haifar da ɓarnar gilashin gaban injin jirgin.

NRC ta nuna matuƙar damuwa kan yadda a cikin makonni biyu da suka gabata aka samu irin waɗannan hare-hare a wurare da dama, ciki har da Gidan Busa/Sarki Gora a yankin Kakau, ƙaramar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, da wasu wurare daban-daban.

A cewar mahukuntan hukumar, an riga an samu irin waɗannan hare-hare a fiye da wurare shida a kan wannan hanya, abin da ke ƙara tsananta ƙalubalen gudanar da ayyukan jiragen ƙasa, tare da barazana ga lafiyar fasinjoji da ma’aikata.

Hukumar ta ƙara da cewa, hare-haren na ci gaba da jefa rayuka cikin haɗari tare da lalata muhimman kayayyakin layin dogo, kana suna zama wani nau’i na taɓarɓarewar tattalin arziki, domin suna iya kawo cikas ga harkokin sufuri na ƙasa da kuma rage tasirin jarin da Gwamnatin Tarayya ta zuba a fannin jiragen ƙasa.

Sai dai duk da wannan matsala, NRC ta tabbatar da cewa har yanzu ana ci gaba da gudanar da zirga-zirgar jiragen ƙasa tare da ɗaukar matakan tsaro masu tsauri, inda ma’aikatan hukumar ke nuna ƙwazo da ƙwarewa wajen tabbatar da cewa fasinjoji sun isa inda za su cikin aminci.

Hukumar ta jaddada cewa haɗin kai tsakanin gwamnati da al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen kare wannan muhimmin fanni na sufuri.

By ukarofi