NSIB: An gano matuƙan jirgi a buge suke bayan Air Peace ya goce yayin sauka a Fatakwal

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Fasinjoji da jami’an jirgin sama sun tsallake rijiya da baya yayin da wani jirgi daga Legas ya goce wa hanyarsa a lokacin da yake ƙoƙarin sauka a filin jiragen sama na Fatakwal.

A yayin saukar ne jirgin ya samu tsaiko daga tazarar mita 2,264 inda ya kuma dakata daga tsawon mita 200, a lokacin da ya goce wa hanyar saukar.

Daga bisani jirgin ya yi nasarar sauka cikin aminci ba tare da samun wani rahoto na rauni daga kowa ba, kamar yadda rahoton ofishin bincike na NSIB ya shaida.

Rahoton ya bayyana cewa, an samu wasu daga cikin jami’an jirgin a buge yayin da al’amarin ya faru sakamakon shan wani abu mai bugarwa da suka yi.

An gano cewa wani kyaftin da jami’i ɗaya sun sha wata giya da aka alaƙanta da sinadarin ‘Ethyl Glucuronide’.

Wannan shi ne ƙalubalen da jiragen ƴan kasuwa ke fuskanta musamman idan aka samu ƙarancin wadataccen gani daga matuƙa ko tsaikon lamuran gudanarwa.

Kamfanin Air Peace ɗaya ne daga cikin kamfanonin jiragen sama da ke zirga-zirga a sassan Nijeriya da wasu ƙasashen duniya kamar su Landon, Saudiyya, Dakar, Freetown da Ghana.

By Babaji