Kano: An buƙaci al’ummar Bichi su yi rajistar katin zaɓe

Spread the love

Shugaban Ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ya kirayi al’umma da ke sassan ƙaramar hukumar da su yi rajistar katin zaɓe da ake gudanarwa a yanzu.

A sanarwar da jami’ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, Sakataren ƙaramar hukumar, Hon Anas Muhammad Abdullahi a madadin ciyaman ɗin ya bayyana haka a yayin tattaunawa da masu ruwa da tsaki a ofishinsa da ke sakatariyar ƙaramar hukumar.

Ya ce, yin rijistar katin zaɓen na da matukar muhimmanci, kasancewar ita ce kaɗai za ta bai wa al’ummar yankin damar kaɗa ƙuri’a a yayin zaɓuka.

Ya bayyana yin rajistar a matsayin sauke nauyin da ke kan kowane ɗan ƙasa na gari, domin samun damar zaɓen shugabannin da ya ke so su jagorance shi bisa gaskiya da adalci a kowane mataki.

Ya kuma ce, zaɓen shugabanni na gari haƙƙi ne da ya rataya a kan al’uma, wanda kuma idan ba da katin zabe ba, mutane suna gani bara-gurbi za su fito su karbe ragamar jagoranci.

Sakataren Mulki na Bichi, ya cigaba da cewa, la’akari da haka, da fara aikin rijistar zabe a fadin jihar nan, shugaban Karamar Hukumar, ya ɗauki duk wasu matakai da suka wajaba don samun nasarar aikin, duba da mahimmancin katin zaɓe ga kowane dan kasa na gari.

“Alhamdu Lillah akwai kwamitoci na musamman, na Kar-Ta-Kwana da Karamar Hukumar Bichi ta kafa, kuma suna nan suna aiki ba dare ba rana domin wayar da kan al’uma domin su fita yin rijistar katin zabe.” In ji shi.

Kazalika, ya bayyana cewa shugaban karamar hukumar a kodayaushe a tsaye yake kan dukkan wani abu da ya shafi inganta rayuwar al’umar yankin.

A nasa ɓangaren, Hakimin Bichi Galadiman Kano, Alhaji Mannir Sanusi, wanda sakatarensa Malam Idris Shitu Malikawa ya yi jawabi a madadinsa, ya ce, duk lokacin da wani abu ya zo na amfanar da al’uma suna ba da gudunmawarsu ta hanyar dagatai da masu unguwanni, tare da yin kira ga al’uma su ba da hadin kai.

By Babaji