Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
An yabawa Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na jihar Katsina bisa ba ƙananan hukumomin jihar damar cin gashin kansu wanda ke ba su damar gudanar da ayyukan raya ƙasa don inganta walwala da jin daɗin al’ummarsu musamman mutanen karkara.
Mai ba gwamnan shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-Gwajo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Katsina.
Sanarwar ta bayyana cewa a baya-bayan nan ƙananan hukumomin sun gudanar da ayyuka daban daban na kawar da zaizayar ƙasa da gyaran cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da ɗakunan shan magani da kuma gyara masallatai da maƙabartu a yankunansu.
“Kwana-kwanan nan kowace ƙaramar hukuma a jihar nan ta samu Naira miliyan 350 domin gudanar da waɗannan ayyukan waɗanda su suka nemi su gudanar da ayyukan, kuma aka basu dama.
“Alal misali kowace ƙaramar hukuma ta samu Naira miliyan 200 na ayyukan kawar da zaizayar ƙasa domin kare gonaki da gidaje da filaye daga zaizayewa, musamman a cikin damina,”inji Gwajo Gwajo.
“Kafin nan kowace ƙaramar hukuma ta amshi Naira miliyon 100 domin gyarawa da faɗaɗa ƙananan asibitoci da ɗakunan bada magani, muna da mazaɓu 361 a jihar nan, an gyara asibiti ɗaya da ɗakin bada magani ɗaya a kowace mazaɓa,”a cewar sa.
Gwajo Gwajo wanda tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Katsina ne ya bayyana cewa an kuma an ba ƙananan hukumomin kuɗi don gyaran makabartu da masallatai da kuma gudanar da addu’o’i na musamman don ɗorewar zaman lafiya a jihar, aƙalla kowace ƙaramar hukuma ta samu jimillar kudi Naira miliyan 30 domin gudanar da waɗannan ayyukan bayan da malaman addini sun buƙaci haka.
“Haka kuma ƙananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro sun amince su riƙa siyan kayan aiki da bada alawus ga ‘yan banga da ‘yan sa-kai, da sauran tallafi domin magance matsalar tsaro a yankunan su,”tsohon kakakin majalisar ya ce.
“Waɗannan kuɗaɗen, ƙananan hukumomin ne suka kashe su da kansu, kuɗinsu ne kuma su ke zartar da shawarar yadda za su kashe su don inganta walwala da jin daɗin al’ummarsu,”.ya faɗi haka.
Gwajo Gwajo ya tabbatar da cewa gwamna Dikko Raɗɗa, duk abin da za ayi, ana yinsa ne bisa doka, shi ya sa ƙananan hukumomi ke da damar kashe kuɗaɗen su bisa ‘yanci da zaɓinsu.
Ya bayyana cewa ƙananan hukumomin ke biyan albashinsu, da alawus alawus, da kuɗaɗen tafiyar da harkar gwamnati, sannan kuma suna gudanar da ayyuka a fannin kiwon lafiya da ilimi, da muhalli da noma, da manyan ayyuka da sauran su domin inganta walwalar al’umarsu.
