
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Kula da Ma’aikata ta Jihar Bauchi, ta tsige Emos Joshua, wanda babban mataimakin jami’in ilimi ne a Kwalejin Gwamnati da ke Azare bisa zargin sa a cin zarafin mace.
Hukumar ta ce, ayyukan jami’in sun saɓa wa saɗarorin sashe na 0327 na kundin dokar ma’aikatan jihar.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis ta Kakakinta Saleh Umar, hukumar ta ce an ɗauki matakin ne a zaman hukumar karo na 32 a ranar 11 ga Satumba, 2025.
Ya ce, tuni aka ɗauki matakin bayan nazari game da ababen da doka ta tanada akan al’amarin.
Haka kuma a yayin zaman aka ƙara wa wasu mataimakan daraktoci guda biyu matsayi zuwa daraktoci a matakin aiki na 16.
Sannan, a wani gefe kuma aka ƙara wa ma’aikatan ungozomanci matsayi su guda 80 daga mataki na 10 zuwa na 14.
