Kotu ta ba DSS damar gaggauta gabatar da shari’ar Al-Barnawi bisa tuhumar kai hari ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya na Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bai wa hukumar tsaro ta farin kaya DSS, damar gaggauta gabatar da shari’ar Khalid Al-Barnawi, wanda ake zargin sanannen ɗan ta’adda ne na Boko Haram da wasu mutane huɗu bisa zargin su da hannu a kitsa bom ɗin da ya tarwatsa ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Abuja a ranar 26 ga watan Agustan 2011.

A yau Juma’a Mai Shari’a Emeka Nwite, ya bayyana hakan a kotun bayan miƙa buƙatar haka da DSS ta yi ta hannun mai kare ta Alex Izinyon (SAN) domin gaggauta kammala shari’ar wadda aka ɗauki tsawon lokaci ana jira, lamarin da ɓangaren masu kare waɗanda aka shigar ƙara suka amince da shi.

A watan Agustan 2011 wani ɗan ƙunar baƙin wake ya yi sanadin kai hari mafi muni a ofishi mallakin ƙasar waje a Nijeriya a karo na farko, inda sama da mutane 20 suka rasu a yayin da sama da 70 suka jikkata.

Harin ya girgiza al’umma a sassan duniya da yin alla-wadai daga MƊD da gwamnatocin ƙasashen waje.

Al-Barnawi, wanda aka san shi da sunaye daban-daban kamar su Kafuri, Naziru, Alhaji Yahaya, Mallam Dauda da Alhaji Tanimu, jami’an DSS sun yi nasarar cafke shi ne a watan Afrilun 2016 a Lokoja, Babban Birnin Jihar Kogi bayan shekaru biyar ana farautar sa.

Da yake gabatar da hukuncin, Alƙali Nwite ya ba DSS damar gabatar da hujjar wata ɗauka ta bidiyo, inda ake sa ran ganin su a ciki a lokacin da suke amsa aikata laifin da ake tuhumarsu a kai.

Alƙalin ya yanke cewa za a gabatar da hujjar ne a lokacin da duka ɓangarorin da ke da alaƙa da al’amarin suka halarci zaman kotun, inda daga nan ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranakun 23 da 24 ga watan Oktoba.

By Babaji