Hukumar SEPA ta ƙaddamar da ba marasa lafiya magani kyauta a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban hukumar kare muhalli ta Jihar Katsina Alh. Kabir Usman Amoga ya ƙaddamar da shirin duba marasa lafiya tare da basu magani kyauta a ƙaramar hukumar Katsina.

Marasa lafiyan maza da mata sama da 500 a firamaren Dutsen Amare dake cikin garin Katsina suka amfana da tallafin magungunan.

A jawabin sa shugaban hukumar kare muhalli ta Jihar Katsina Alh. Kabir Usman Amoga ya bayyana cewa” yayi wannan ƙoƙari ne domin tallafama al’umma musamman mabuƙata duba da irin halin da ake ciki.

Amoga ya bayyana cewa idan kaje asibiti za kaga al’umma mabuƙata amma kuɗin abin sayen magani ya gagara, “shine mukayi tunanin zuwa da taimako domin tallafama masu,”inji shugaba SE PA.

Ya ce wannan shiri zai gudana har tsawon kwanaki (3) ga masu fama zazzaɓin cizon sauro, Typhod, da kuma mura inda zasu zo a duba su a kuma basu magani kyauta.

A nasa jawabin babban baƙo a wurin taron kwamandan Hisba ta Jihar Katsina Dr. Abu Ammar yayi yabo da jin jina ga Alh. Kabir Usman Amoga bisa wannan abun alkairi da ya shirya tare da roƙon Allah ya saka masa da alkairi.

Itama a na ta jawabin shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Katsina SEMA Haj.Binta Dangani ta yabama Alh. Kabir Amoga bisa wannan abu da yayi wanda ya gada a wurin uban gidan sa mai girma gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa.

Shugaban ƙaramar hukumar Katsina wanda ya samu wakilcin mataimakin sa Hon. Yusuf Saulawa ya yabama Alh Kabir Amoga bisa wannan ƙoƙari wanda haƙƙin su suyi amma yayi masu tare da roƙon Allah ya saka masa da alkairi.

By ukarofi