Karuwar bashin da Nijeriya ke ci abin damuwa ne – Tajuddeen Abbas 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya nuna damuwa kan yadda bashin Nijeriya ya ƙaru zuwa Tiriliyan 149.39  a farkon 2025, kwatankwacin dala biliyan 97, wanda ya wuce iyakar kashi 40 da doka ta gindaya, inda ya kai kashi 52 na GDP.

Abbas ya bayyana haka ne a taron shekara-shekara na ƙungiyar WAAPAC a Abuja, yana mai cewa hauhawar bashin na barazana ga ɗorewar tattalin arziki, tare da gargaɗin cewa rancen da ke tallafa wa cin hanci da ciyar da buƙatu bai kamata a ci gaba da shi ba.

Ya ce dole rance ya kasance domin ayyukan raya ƙasa kamar hanya, lafiya, ilimi da masana’antu.

Abbas ya kuma bayyana shirye-shiryen Nijeriya na jagorantar kafa tsarin sa ido kan bashin majalisun dokoki a Yammacin Afirka domin tabbatar da gaskiya da tsari.

Kakakin ya jaddada cewa Majalisa za ta tabbatar da amincewar jama’a kafin karɓar manyan rance, tare da sauƙaƙa rahoton bashi ga ‘yan ƙasa, domin inganta gaskiya da dorewar tattalin arziki.

By ukarofi