
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Ƙungiyar Ƴan jarida ta Ƙasa, NUJ reshen jihar Bauchi ta bayyana alhininta game da rasuwar Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammadu Ɗan-Yaya inda ta ce mutuwarsa rashi ne ga ƙasa baki ɗaya.
Ta aika saƙon ta’aziyyarta ga gwamnatin jihar Bauchi, Majalisar Sarakuna, Masarautar Ninga da ma al’ummar jihar da su jure babban rashin tare da yi masa addu’ar fata samun rahamar Allah.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta hakaito irin gudunmawar da Sarkin ya bayar wajen samun ci gaba a ɓangaren al’adu musamman a Arewacin Nijeriya da ƙoƙarinsa ta fannin zaman lafiya da haɗe kai tsakanin gwamnatoci.
Haka kuma NUJ ta aika saƙon ta’aziyyarta ga iyalan wasu mambobinta guda biyu, Aliyu Jibo da Babangida Mohammed waɗanda suka rasu a ranar Lahadi bayan fama da jinya inda ƙungiyar ta ce rasuwarsu rashi ne ga aikin jarida, ta na mai yi mu su addu’o’in samun rahamar Allah.
