NUPENG ta dakatar da yajin aiki bayan DSS ta shiga tsakani

Spread the love

Ƙungiyar masu dakon man fetur (NUPENG) ta dakatar da yajin aikin da ta fara bayan cimma yarjejeniyar da hukumomin matatar Ɗangote.

A ranar Litinin ƙungiyar ta fara yajin aiki domin nuna damuwarta kan matakin kamfanin Ɗangote na ƙin barin ma’aikatan matatarsa shiga cikin ƙungiyar.

A wani saƙo da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa yarjejeniyar da suka cimma da matatar ɗangote da sauran rukunonin kamfanin ita ce za a bai wa direbobin manyan motocin dakonsu damar shiga ƙungiyar bisa raɗin kansu, matakin da matatar ɗangoten ke adawa da shi da ya haifar da taƙaddamar.

Yajin aikin ya haifar da fargabar samun ƙarancin man fetur a sassan ƙasar.

An shawo kan ƙungiyar ne bayan tattaunawar sulhu ta kwana biyu da Ministan Ƙwadago, Muhammad Dingyaɗi ya jagoranta tare da haɗin-gwiwar hukumar tsaro ta farin kaya DSS, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Hukumomin matatar sun amince cewa ma’aikatansu na da damar yin ƙungiya.

By Babaji