Gwamnatin Kano ta jaddada gaskiya da riƙon amana a mulki

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa gaskiya da rikon amana sune ginshiƙan da ta gina mulkinta a kai, tana mai cewa waɗannan halaye ne ke tabbatar da ingantaccen shugabanci da ɗorewar ci gaba.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana haka a Kano yayin ganawa da manema labarai. Ya ce isar da bayanai cikin gaskiya da lokaci ga jama’a kan manufofi, ayyuka da shirye-shiryen gwamnati na daga cikin manyan al’amuran da ke tabbatar da nagartaccen mulki. Ya kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai su kasance masu bin ƙa’idoji na aikin jarida ta fuskar adalci da gaskiya.

Waiya ya koka kan rahotannin da ake maimaitawa a wasu kafafen yaɗa labarai kan jami’an gwamnati, yana mai cewa rahotannin na da nufin ɓata sunan gwamnatin Abba Kabir Yusuf duk da cewa wasu daga cikin batutuwan suna gaban kotu. Ya ce hakan ba ya taimaka wa jama’a sai dai ya jawo ruɗani.

Kwamishinan ya jaddada irin sauye-sauyen da gwamnatin ta yi domin ƙarfafa gaskiya a harkokin kuɗi da aiwatar da ayyuka. Daga cikin muhimman matakan akwai aiwatar da dokar saye da sayarwa ta jihar Kano ta 2021, gudanar da binciken tsare-tsare lokaci-lokaci, da kammala tsarin dijital na Kano State Integrated Monitoring System (KSIMS) da zai bai wa gwamnati damar sa ido kan ayyuka a zahiri.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati na wallafa bayanan kowane aiki da majalisar zartarwa ta amince da shi a kafofin sada zumunta da kafafen da na jaridu domin jama’a su san yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati. Haka kuma, Hukumar Karbar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci (PCACC) na aiki ba tare da tsoma bakin ’yan siyasa ba.

Kazalika Waiya ya tabbatar da cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta ci gaba da gina tubalin nagartaccen mulki bisa gaskiya da riƙon amana domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa da jin daɗin al’ummar Kano.

By ukarofi