
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Hukumar kula da ɗalibai masu yi wa ƙasa hidima, NYSC ta yanke shawarar bai wa wasu ƴan hidimar ƙasa satifiket bayan sun kasance a hannun ƴan bindiga tun a shekarar da ta gabata.
A ranar 17 ga watan Agusta, 2023 ne a lokacin da ɗaliban ke kan hanyarsu ta zuwa Sakkwato domin karɓar horon mako uku gabannin fara hidimar inda a nan ƴan bindiga suka yi garkuwa da su.
Ɗaliban waɗanda su takwas ne, sun taso ne daga jihar Akwa-Ibom da ke Kudu-maso-gabashin Nijeriya a motar kamfanin jihar (AKTC) inda suka yi artabu da ƴan bindiga a yankin jihar Zamfara.
A lokacin da ya ke jawabi wa manema labarai, Darakta-Janar na NYSC, Burgediya Janar Yushau Ahmed ya ce za a bai wa kowannen su shaidar kammala hidimar ƙasa.
Ya ce, kasancewar sun fuskanci wahalhalu a hannun ƴan ta’addar, ba sai sun yi wata sabuwar hidima ba don haka za a sallame su tare da takwaransu da suka samu damar yin hidimar.
Ya ƙara da cewa, rundunarsu tare da haɗin gwiwar jami’an ƴan sandan farin kaya ta DSS ne suka ceto ɗaliban a lokuta mabanbanta ba tare da biyan kuɗin fansa ba.
Bugu da ƙari, ya ce babu ɗaya daga cikin ƴan ta’addan da aka kama, sai dai an yi nasarar kashe wanda ya jagoranci yin garkuwa da ɗaliban.
