
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ofishin jakadancin Nijeriya a birnin Johannesburg ya aike da saƙon kira ga aminci ga ‘yan Nijeriya da ke zama a yankin Kempton Park da kewayen Ekurhuleni, bayan mutuwar wasu mata guda takwas da ofishin ya ce rundunar ‘yan sandan Afirka ta Kudu (SAPS) tana bincike a kai.
Rahotanni sun bayyana cewa, Ofishin a sanarwar da ya fitar a ranar Laraba, 16 ga Satumba, 2026, ya ce mace-macen sun faru ne kusan watanni biyu da suka gabata kuma hakan ya sa aka gaggauta kafa kwamitin bincike da ya haɗa jami’an hukumomin tsaro daban-daban.
A cewar ofishin, masu bincike sun gano cewa mutuwar matan na da alaƙa da juna ta fuskar dalilan da suka haifar da su, sannan da wane hali za a iya danganta su. Saidai jami’an na SAPS ba su bayyana cewa wani ɓangare ɗaya ne yake da alhakin kisan ba ki kuma ba a tabbatar da hannun wani makashi ba a ciki.
Amma ofishin jakadancin ya ce, ana cigaba da bincike domin gano haƙiƙanin yadda al’amarin ya auku, sannan yana ankarar da ‘yan Nijeriya mata da ‘yan mata masu zama ko karatu ko ma tafiye-tafiye da su kasance masu kula da ƙoƙarin kiyaye shiga wurare masu haɗari. Sannan, ofishin ya bayyana cewa, ƙididdiga ba ta fitar da wani alaƙa tsakanin mutuwa takwas ɗin ba da wani salon aikin laifi.
Akan haka ne ya shawarci al’umma musamman mata da su nisanci yin tattaki ko motsa jiki su kaɗai a keɓance ko wasu wurare da ba a saba da su ba, ciki har da buɗaɗɗun filaye ko yankunan da babu jama’a.
Kazalika, ta buƙaci ‘yan Nijeriya da su riƙa tafiye-tafiye a cikin tawaga idan hakan zai yiwu, sauya hanya da la’akari da lokaci da kuma ƙaurace wa amfani da keɓaɓɓun wurare domin kasantuwar su cikin aminci yayin cigaba da yaƙi da halin ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu.
+27627642412, da adireshin Imel: [email protected], sune za a yi amfani da su wajen aike wa ofishin saƙo domin muhimman al’amuran da suka shafi mata mazauna ƙasar.
