
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Amurka ta ce za ta dakatar da bada wasu nau’ukan bizozin shiga ƙasar ga ƴan Nijeriya daga ranar 1 ga watan Junairu, 2026 biyo bayan sabon matakin da fadar shugaban ƙasar ta ɗauka akan tsaron iyakoki da ƙasa.
A ranar Litinin ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya sanar da cewa matakin zai fara aiki ne daga ƙarfe 12:01 na dare, kamar yadda fadar White House ta bayyana.
Sanarwar ta ce, Nijeriya tana ɗaya daga cikin ƙasashe guda 19 da sabon tsarin ya shafa. Sauran sun haɗa da Angola, Antigua da Barbuda, Benin, Burundi, Cote D’Ivoire, Kuba, Dominica, Gabon, The Gambia, Malawi, Mauritania, Senegal, Tanzania, Togo, Tonga, Venezuela, Zambia da kuma Zimbabwe.
Nau’ukan bizozin da al’amarin ya shafa sun haɗa da nonimmigrant B-1/B-2 na masu ziyara, sai F, M da J na ɗalibai da masu ziyara na ‘exchange visitor’. Haka kuma, ya shafi na masu zama na wucin-gadi.
A cewar ofishin jakadancin, dakatarwar ba ta shafi kowa ba inda ta ware waɗanda aka bai wa mafaka sakamakon tsangwamar ƙabilanci ko addini da wasu tsirarun mutane ke fuskanta a Iran da ƴan wasu ƙasashe da al’amarin bai shafa ba da kuma ma’aikatan ƙasar da ba ƴaƴanta ba.
