
Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya yi barazanar shigar da ƙarar cin mutunci ta kuɗi har biliyan N100 akan wani ɗan kasuwa da ke Jihar Kaduna mai suna Injiniya Kailani Mohammed, bisa zargin sa da ɓata masa suna da yin kalaman batanci a bainar jama’a.
Ɗangote ya bada wa’adin kwanaki bakwai ga Injiniyan da ya janye kalaman nasa tare da bayar da cikakken bayani da kuma neman afuwa a fili, ko kuma ya fuskanci matakin shari’a.
Hakan na kunshe ne a wata takarda da lauyan Ɗangoten, Dakta Ogwu James Onoja, SAN, na kamfanin Onoja Law Firm da ke Abuja ya fitar, inda attajirin ya zargi ɗan kasuwar da yin kalaman ƙarya da suka rage martabarsa tare da ɓata sunan kasuwancinsa, musamman ta hanyar zargin cewa ya yi “haramtattun kasuwanci” a Fatakwal ta Jihar Ribas, a shekarun 1980s.
Lauyan Ɗangote ya bayyana cewa kalaman sun ƙalubalanci sahihancin dukiyarsa da kuma mutuncin harkokin kasuwancinsa, lamarin da ya ce yana da illa ga suna da amincewar da Dangote ya gina tsawon shekaru a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.
An ruwaito cewa, kalaman da ake ƙorafi a kai Injiniya Kailani Mohammed ya furta su ne a wata hira ta tashar TrustTV News a ranar Laraba, 17 ga Disamba, 2025, yayin da yake mayar da martani kan koken da ya shigar gaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) akan Dakta Farouk Ahmed, tsohon shugaban NMDPRA.
