
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Al’umma a garin Zak da ke Gundumar Bashar ta Ƙaramar Hukumar Wasen Jihar Filato sun shiga damuwa da tashin hankali a sakamakon garkuwa da kimanin matafiya 28 da wasu ƴan bindiga suka yi a daren ranar Lahadi wayewar Litinin.
Waɗanda aka sacen sun haɗa da maza, mata da kuma yara, inda al’amarin ya rutsa da su a lokacin da suka taho daga Ƙauyen Zak zuwa Sabon Layi domin halartar taron Maulidi.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho ga manema labarai, wani shugaban matasa a Wase mai suna Shafi’i Sambo, ya ce matafiyan sun gamu da ƴan bindigar ne da misalin ƙarfe 8 na dare a waje da garin.
A cewarsa, maharan sun samu damar tsayar da motar fasinjojin a lokacin da suka haɗu da su tare da kwashe baki ɗayansu zuwa cikin jeji, inda suka bar motar matafiyan a wajen.
Ya bayyana cewa, motar da ta yi jigilar mutanen ta wani jagoran al’umma ne Zak, sannan kasancewar akwai sanannun mutane acikin fasinjojin hakan ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da ɗimuwa.
Wani mazaunin yankin mai suna Ibrahim Bashar Musa, ya ce an gano faruwar al’amarin ne a safiyar ranar Litinin, a lokacin da wasu matafiya suka riski motar da aka kwashe waɗancan mutanen fake a gefen hanya.
Kazalika, Sambo ya bayyana cewa tuni aka sanar da hukumomin tsaro tare da kira a gare su da su gaggauta ceto waɗanda abin ya shafa cikin aminci.
