
Gwamnatin Tarayya ta ce ta amince da shirin gwajin ƙwaya ga masu neman aikin gwamnati a faɗin Nijeriya, inda ta ce daga yanzu za a saka gwajin ta’ammali da ƙwaya a cikin abubuwan da suka zama wajibai kafin a ɗauki mutum aiki a ƙasar.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren Gwamnatin Tarayya, Segun Imohiosen ya fitar a madadin gwamnatin.
Ya ce, “don haka ana umartar dukkan manyan sakatarori da shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya a ƙasar da su saka gwajin ƙwaya a cikin abubuwan da ake buƙata kafin samun aikin gwamnati.”
Sanarwar ta ƙara da cewa, hukumomin ƙasar za su haɗa hannu da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) domin samun nasarar wannan aiki.
Ya bayyana cewa, ɗaukar wannan matakin ya zama dole ne bayan yawaitar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, “musamman a tsakanin matasa a ƙasar nan.”
Haka kuma, matakin wani ɓangare ne na matakan daƙile ayyukan ta’ammali da miyagun ƙwayoyi na dabarun gwamnatin tarayya a 2025.
Tun a watan Nuwamba ne Hukumar Kwastom ta gabatar da gwajin ƙwaya a,matsayin wajibi ga masu neman aiki a ƙarƙashinta domin ƙarfafa horo da inganta ayyukan tsaron iyakoki.
