Ondo: Yadda sarki ya ciji takwaransa a kunne

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rahotanni daga Jihar Ondo sun bayyana cewa an samu fargaba a garin Igbokoda dake Ƙaramar Hukumar Ilaje ta jihar biyo bayan farmakin da wani babban sarki (Oba Oladimeji) ya kai wa sarkin ƙauyen.

Daily Post ta ruwaito cewa, an farmaki sarkin ne gabannin buɗe titin Igbokoda-Okitipupa mai tsawon kilomita 27.5 a garin sarkin, wanda wani babban sarki daga cikin sarakunan yankunan jihar zai ƙaddamar.

Zuwa lokacin kammala rahoton, ba a bayyana sunan sarkin da ya ciji kunnen sarkin gargajiyar ba, inda a ranar Talata ne mata a garin suka yi zanga-zanga da bayyana rabin jikkunansu a waje.

Muryoyi sun ce, an fara rikici ne a lokacin da wani masanin shari’a (Oba Odidiomo) ya nemi jagoran ƙauyen da ya tashi daga sahun kujerun layin gaba waɗanda an ware su ga manyan sarakunan gargajiya, amma ya ƙi bin umarnin.

Lamarin da ya haifar da cacar baki a tsakaninsu, wanda ya kai su ga kokowa da raunata sarkin bayan da wasu sarakuna da sauran baƙi suka shiga tsakani.

Daga lokacin ne aka garzaya da shi asibiti cikin gaggawa domin ba shi kulawa.

Wani mataimaki ga sarkin da ya nemi a sakaye sunansa, ya ce sarkin da ya yi cizon, ya yi hakan ne duba da cewa yana da kusanci da wani babban jami’in gwamnati.

By Babaji