
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Talata ne Gwamna Umar Bago na Jihar Neja ya yi afuwa ga wasu fursunoni guda 11 da aka yanke wa hukuncin kisa a jihar.
Babbar Kotun Minna ta yanke musu hukuncin bisa bisa hannu a laifin kashe-kashen da aka yi a faɗan ƙabilanci a Ƙaramar Hukumar Lavun ta jihar.
A yayin ganawa da manema labarai a Minna, Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a na jihar, Nasiru Muhammad Mu’azu ya sanar da hakan, inda ya ce gwamnan ya yi amfani da ikonsa ne da dokar ƙasa gyaran 1999 sashe na 212 (1) ta ba shi dama wajen yin yafiyar ga mutanen.
Hakan ya biyo bayan saƙon roƙo da suka aika wa gwamnan da ofishin antonin.
Kwamishinan ya ce, bayan nazari da majalisar mashawarta ta yi kan al’amarin, gwamnan ya yanke shawarar yi wa fursunonin afuwa.
