Operation Kano Tsaf-Tsaf: REMASAB ta fara sayen leda da robobin ruwa domin inganta tattalin arziki a jihar

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

A ci gaba da ƙoƙarin inganta harkar sarrafa shara (recycling) da tallafawa masu tsintar kayan amfani a bola, hukumar REMASAB ƙarƙashin jagorancin Manajan Darakta, Dr. Muhammad S. Khaleel, ta ƙaddamar da shirin siyan ledojin pure water, robobin ruwa, ledojin indomie, da sauran kayan amfani da za a iya sake sarrafawa.

Shirin, wanda ya hada da masu aikin tsintar shara, matasa marasa aikin yi, mata masu zaman gida, da dalibai, na nufin samar da sahihin hanyar dogaro da kai ga al’umma tare da rage zaman banza a faɗin jihar.

A cewar hukumar, tsarin biyan sakamakon kayayyakin da ake kawo wa ya kasance kamar haka: za a duba nauyin kayan, sannan a biya mai kawosu ta hanyar kayan masarufi irinsu madara, man gyaɗa, Indomie, sabulu, man shafawa, da sauran su bisa ga nauyin da aka auna.

REMASAB ta bayyana cewa wannan shiri yana daga cikin matakan da suke ɗauka don inganta rayuwar al’ummar Kano, da kuma tallafawa manufofin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na samar da hanyoyin dogaro da kai da kuma rage zaman banza.

Hukumar ta yi addu’ar samun nasara ga dukkan shirye-shiryen da ake gudanarwa da goyon bayan gwamnatin jihar.

By ukarofi