Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP a Jihar Gombe kuma mai neman tikitin takarar gwamna, Alhaji Abdulkadir Hamma Saleh, ya bayyana aniyarsa ta ƙalubalantar matakin bai wa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami tikitin takarar gwamna a kotu.
Hamma Saleh ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke Gombe, inda ya ce ba zai amince da abin da ya kira rashin bin ƙa’ida da tauye haƙƙin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar ba.
Ya ce shi da sauran masu neman tikitin gwamna sun shafe shekaru suna bautawa jam’iyyar PDP da kuma jajircewa wajen gina ta, saboda haka bayyana Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar ba tare da cikakken bayani ko bin tsarin da ya dace ba abin damuwa ne.
A cewarsa, ya sayi fom ɗin neman takarar gwamna kuma ya bi dukkan ƙa’idojin da jam’iyyar ta shimfiɗa, amma daga baya kawai suka ji an bayyana sunan Pantami a matsayin wanda zai ɗauki tutar PDP a zaɓen 2027.
“Mu ba mu da wata masaniya da muka samu dangane da shigowar Pantami cikin PDP kafin a bayyana shi a matsayin ɗan takara. Wannan abu ya tayar da ƙura sosai a cikin jam’iyyar,” inji shi.
Jigon na PDP ya ce zai bi duk hanyoyin da doka ta tanada domin kare haƙƙinsa da kuma tabbatar da an yi adalci ga mambobin jam’iyyar da suka tsaya tsayin daka tun farko.
Ya kuma bayyana Pantami a matsayin wanda aka fi sani da kasancewa babban jigo a jam’iyyar APC, yana mai cewa a baya ya nemi takarar gwamna a ƙarƙashin APC amma bai samu nasara ba.
“Idan shi yana ganin ba a yi masa adalci a APC ba, to mu ma muna da haƙƙin a yi mana adalci a PDP,” in ji Hamma Saleh.
Maganar tasa na zuwa ne a lokacin da batun bai wa Pantami tikitin takarar gwamna a PDP ke ci gaba da haifar da cece-kuce da muhawara a tsakanin mambobin jam’iyyar da masu bibiyar siyasar Jihar Gombe.
Tsohon Ministan Sadarwa a Nijeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya samu tikin takarar gwamnan Gombe a jam’iyyar PDP bayan da ya koma cikinta. Ya yi nasarar ne lokacin zaɓen fitar da ‘yantakara da aka yi yau a wani wajen taro a jihar Gombe.
Shugaban kwamitin zaɓe na PDP, Hon Gregory Yenlong ne ya ayyana fitaccen malamin addinin a matsayin ɗantakara ɗaya tilo a wani.
Da yake magana jim kaɗan bayan ayyana shi a matsayin wanda zai yi wa PDP takarar gwamna, Farfesa Pantami ya ce hidimta wa al’ummar Gombe ne ya sa yake neman kujerar gwamnan jihar. Ya yi alƙawari cewa idan har aka zaɓe shi a 2027, zai yi shugabanci bisa gaskiya da adalci. A halin da ake ciki, Pantami zai fafata da wasu ‘yantakarar a zaɓen an 2027, ciki har da Jamilu Gwamna na APC mai mulkin jihar.
Tun farko Farfesa Isa Pantami ya janye daga takarar gwamna a APC bisa zargin ‘maguɗi’ da ‘son rai’ da ya ce sun saɓa da dokokin zaɓen Nijeriya na 2026, kuma ya yi haka ne bayan tuntuɓa da kuma duba na tsanaki na yadda tsarin zaɓen fitar da gwanin yake.
Da ma dai Farfesa Pantami ya shaida cewa bai aminta da sulhun da aka yi a baya ba, wanda ya fitar da Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar ta Gombe kuma ya sha alwashin “yaƙar zalunci bisa doka.”
