Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yanke hukuncin cewa wajibi ne jadawalin zaɓe da Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC) ke fitarwa ya yi daidai da tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026.
Kotun ta kuma tabbatar da cewa INEC na da ikon tsara jadawalin gudanar da zaɓe da kuma yin gyare-gyare a kansa idan buƙatar hakan ta taso, amma dole ne duk wani jadawalin ya kasance cikin iyakokin da dokar zaɓe ta shimfiɗa.
Mai shari’a James Omotosho ne ya yanke hukuncin yayin sauraron ƙarar da jam’iyyar SDP ta shigar kan INEC, inda jam’iyyar ta ƙalubalanci wa’adin da hukumar ta sanya wa jam’iyyun siyasa kafin zaɓen 2027.
Kotun ta bayyana cewa INEC ba ta da ikon rage wa’adin kwanaki 120 da doka ta bai wa jam’iyyun siyasa domin miƙa sunayen ‘yan takararsu, haka kuma ba za ta iya rage wa’adin kwanaki 90 na janye ko sauya ɗan takara ba.
Sai dai kotun ta amince cewa hukumar na da ikon neman kundin rajistar mambobin jam’iyyu da kuma sanya wa’adin gudanar da zaɓukan fidda gwani.
Hukuncin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wata Kotun Tarayya a Abuja ta soke wasu sassan jadawalin INEC na zaɓen 2027, tana mai cewa sun saɓa wa Dokar Zaɓe ta 2026.
Bayan hukuncin, INEC ta ɗaukaka ƙara tana neman Kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin, tana mai cewa tana da ikon tsara jadawalin da zai tabbatar da bin dokar zaɓe.
Masana harkokin siyasa da ƙungiyoyin fararen hula dai sun yi maraba da hukuncin kotun, suna masu cewa ya tabbatar da cewa babu wata hukuma da ta fi ƙarfin doka a tsarin dimokuraɗiyya.
