
Daga BELLO A. BABAJI
Wani rahoto da Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) ta fitar a ranar Laraba, ya tono yadda aka samu cin zarafin ƴan ɗan-adam daga ƙungiyoyin ƴan ta’adda a yankin Kudu maso Gabas na Jamhuriya Afirka ta Tsakiya, waɗanda musamman hare-hare ne da suka fi shafar inda al’ummar Musulmi suke da kuma ƴan gudun hijira na ƙasar Sudan.
Binciken da ofishin ƴancin ɗan-adam na MƊD (OHCHR) ya da na jami’an wanzar da zaman lafiya a ƙasar, MINUSCA, ya bayyana hujjoji na kashe-kashe da cin zarafin ƴan’uwa mata da kuma duka.
Sauran sun haɗa da tsangwamar su da tilasta masu yin ayyukan ƙwadago gami da sace-sace a gidaje da shaguna.
A tsawon shekaru da dama ƙasar ta na fama da matsalolin rashin zaman lafiya da rikicin ƙabilanci da na addini.
Binciken na MƊD’n ya kuma nuna cewa, akan samu mutum ɗaya cikin biyar da ya rasa matsuguninsa a sanadiyyar rikice-rikicen da ke faruwa a ƙasar.
Lamarin ya haifar da tsaiko ga harkokin ababen more rayuwa da makamantansu a wurare da suka haɗa da makarantu da asibitoci.
Yaƙin Sudan da zaman ɗar-ɗar a Kudancin Chadi sun yi sanadin al’umma sun zama ƴan gudun hijira da neman mafaka da wasu da ke koma wa wasu yankunan Afirka ta Tsakiya.
Hare-hare a yankunan ƙasar sun yawaita da yin sanadin mutuwar mutane da dama da ɗaiɗaita wasu gami da asarar dukiyoyi da dama.
