Rainbow Coalition: APC ta buƙaci Wike ya shiga jam’iyyar

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu shugabannin jam’iyyar APC a jihohi sun yi watsi da ƙungiyar Rainbow Coalition da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ke jagoranta, inda suka buƙaci ya koma APC gaba ɗaya idan da gaske yake goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

A kwanakin baya ma, Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya ce Wike ba zai iya kasancewa yana goyon bayan APC a matakin shugaban ƙasa, yayin da yake tallafa wa ’yan wasu jam’iyyu a zaɓen gwamnoni da ’yan majalisa ba.

Ya ce Wike ya kamata ya zaɓi ɓangare guda, ko ya shiga APC ko kuma ya ci gaba da kasancewa a wajen jam’iyyar.

Haka kuma, shugabannin APC na Imo, Gombe, Ondo, Anambra, Kwara, Plateau da Nasarawa sun yi kira ga Wike ya shiga APC tare da rusa tsarin Rainbow Coalition.

Sai dai Jigawa APC ta ce za ta marabci Wike idan ya yanke shawarar shiga jam’iyyar, tana kuma yabawa goyon bayan da yake bai wa Tinubu.

A wasu jihohi, ciki har da Osun da Delta, shugabannin APC sun ce batun matsayin Wike da Rainbow Coalition ya kamata a bar shi ga shugabancin jam’iyyar na ƙasa.

Wike, wanda har yanzu ɗan PDP ne, ya kare tsarin Rainbow Coalition, yana cewa ba tsarin APC ba ne, kuma manufarsa ita ce tallafa wa Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yayin da sauran jam’iyyu za su iya fafatawa a zaɓen gwamnoni da ’yan majalisa.

Ya kuma jaddada cewa “siyasa ta gari ce”, don haka ya kamata ’yan siyasa su samu damar yin ƙawance bisa yanayin siyasar jihohinsu.

By ukarofi

Leave a Reply