Ramadan: Dujiman Katsina ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su guji tsauwala farashin kayan masarufi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban kwamitin harkokin cikin gida na majalisar wakilai kuma Dujiman Katsina Hon Abdullahi Aliyu Ahmed yayi kira ga ‘yan kasuwa da su guji tsauwala farashin kayan masarufi a cikin watan Ramadan.

Ɗan majalisan yayi wannan kira ne a saƙon sa ga al’ummar Musulmi da shiga watan Ramadan,yace tsauwala farashin kayan masarufi a wannan wata mai tsarki ya saɓa da koyarwar addinin Musulunci.

A wata takardar sanarwar ɗauke da sa hannun mataimaki na musamman kan yaɗa labarai Mr Francis, Sardaunan Dujiman ya ce a wannan wata da al’ummar Musulmi ke gudanar da azumin watan Ramadan abin takaici wasu ‘yan kasuwa lokacin ne suke tsauwala farashin kayan masarufi.

Ahmed mai wakiltar mazaɓar Musawa da Matazu a majalisar wakilai ya kuma kira ga al’ummar musulmi na ƙasa musamman a jihar Katsina da suyi amfani da wannan wata mai tsarki don gudanar da addu’ar samun zaman lafiya a jihar.

Ya bayyana cewa ƙasar nan na neman addu’ar musulmi musamman cikin wannan wata mai darajar, akan haka ɗan majalisar ya ƙara kira ga Musulmin ƙasar nan da su cigaba da gudanar da addu’ar samun zaman lafiya da cigaban ƙasa.

Ɗan majalisar ya tabbatar wa al’ummar mazabar sa na cigaba da aiwatar da ayyukan cigaba a yankin.

Ya nuna jin daɗin sa kan yadda zaman lafiya ke samuwa a yankin da wasu ƙananan hukumomi da suke fama da rashin tsaro.

“Wannan kuwa bai rasa nasaba da jajircewa na gwamna Dikko Raɗɗa da yake yi domin shawo matsalar”inji Dujiman Katsina.

By ukarofi