A ranar Litinin ɗin da ta gaba, Fadar Kremlin ta ƙaryata rahotannin da ke nuni da cewa Asma al-Assad, matar tsohon shugaban Syria Bashar al-Assad, haifaffiyar ƙasar Birtaniya, tana son a raba aurensu.
Rahotanni sun kuma ce tana son barin Rasha.
Dmitry Peskov, mai magana da yawun Kremlin, shi ma ya musanta rahotannin da ke nuna cewa an tsare Assad a Moscow kuma an riƙe da ƙadarorinsa.
Peskov ya ce: “A’a ababen da ake faɗa ko kaɗan ba su yi dadai da gaskiyar lamarin ba,” ya faɗa a lokacin da aka tambaye shi a wani kiran haɗaka kan ko rahotannin gaskiya ne.
An zargi matar mai suna Asma al-Assad, da maka mijin nata a kotu don neman raba aurensu, tare da neman komawarta Burtaniya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni da dama suka bayyana cewa, mijinta, Bashar al-Assad, na fuskantar takunkumi bayan da aka ba shi mafaka a Rasha.
Jaridar Jerusalem Post da ke da rassa a Turkiyya da Larabawa, ta nakalto cewa, Asma ta miƙa buƙatar neman saki ga wata kotun ƙasar Rasha, kuma yanzu haka tana zaman jiran amincewar ta, don ta koma Birtaniya.
Asma wadda ta kasance haifaffiyar Burtaniya, don haka tana da shaidar zama ‘yar ƙasa, baya ga shedar Syria da take da ita, domin kuwa ta yi shekarun farkonta a Landan tare da iyayenta ‘yan Syria.
Rahoton ya ce, ta koma Siriya a shekara ta 2000 kuma ta auri Bashar al-Assad a wannan shekarar.
Ma’auratan sun haɗu ne a lokacin da Assad ke karatu a Landan, inda Asma ke aiki a JP Morgan.
Asmau ta fuskanci ƙalubale na rashin lafiya, ciki kuwa har da fama da cutar daji har karo biyu. A baya-bayan nan an gano tana ɗauke da cutar sankarar bargo, wato leukemia, a watan Mayun wannan shekara, bayan ta ci galaba kan cutar sankarar nono a shekarar 2019.
Hukumomin Rasha sun riƙe ƙadarorinsa da aka ce sun haɗa da zinare kilogiram 270, dala biliyan 2, da kuma gidaje 18 na Moscow, inji rahoton
