Rashin fansho da giratuti ya mayar da tsaffin ma’aikata tamkar mabarata

Daga ZAHRADDEEN IBRAHIM KALLAH

Wata babbar masifa da take neman zama ruwan dare a ƙasar nan shi ne, yadda gwamnatoci ke wulaƙanta ma’aikata tare da danne musu haƙƙoƙinsu. Abin takaicin da ya fi fitowa ƙarara shi ne yadda ma’aikata da suka gama aiki suke zama tamkar mabarata. 

A yayin da suka ƙarar da ƙarfinsu wajen bauta wa ƙasarsu, tare da tunanin samun haƙƙoƙinsu don shirya rayuwa kafin ta Allah ta kasance, a lokacin ne wasu a can gefe za su yi babakere da kasafta waɗannan kuɗaɗe ko haƙƙoƙi. 

Ire-iren waɗannan tsofaffin ma’aikata suna cikin matsananciyar buƙatun rayuwa, amma sun kwashe shekaru kuɗaɗensu babu su, babu labarinsu. Rashin tsarinmu da lalacewar ya yi yawan da sai dai a ce Innalillahi Wa’ina Ilaihir Rajiun. 

Waɗanda suke jagorori ko kan gaba a haifar da wannan matsala da yawansu ko dai ma’aikatan dake kan ganiyar aikinsu ce, ko kuma waɗanda sun yi ritaya tare da shiga siyasa; wanda hakan ya ba su dammar shugabantar al’umma. 

Hadisi ne na ma’ailki cewa idan mutum ya yi maka aiki, kafin gumin jikinsa ya bushe, ka tabbata ka biya shi haƙƙinsa. Amma abin da yake faruwa, shugabannin da ludayinsu yake kan dawo, sun manta da wannan hadisi tare da mayar da waɗannan haƙƙoƙi tamkar kuxaɗen iyayensu. Ai ko da kuɗin iyayensu ne, idan har ya zamo akwai haƙƙin wani a ciki, dole a biya shi cikin gaggawa.

Mu na zaton irin bala’in da yake zagaye da mu ba shi da nasaba da irin waɗannan haƙƙoƙi da ake dannewa? Shin me ya sa ƙasashen Turai da ake kafirci suka zamo abin sha’awa a gare mu, tare da samun ingantacciyar rayuwa da koyaushe ana bada misali da su? Shin ba a gurinsu muka aro wannan dimokaraɗiyar da muke yi ba ne? Me ya sa muka gaza taka birki ga azzalumai irin waɗanda ke danne haƙƙoƙin tsofaffun ma’aikata? 

Mutum ya kwashe shekata 30 ko 35 yana aiki, amma idan ya kammala sai karvar haƙƙinsa ya zama jidali. Ta kai cewar idan har kana son kuɗinka ya fito, sai ka ajiye wani kaso na kuɗin, ba wai a cire a cikin kuɗin ba, a’a za ka ajiye awalajar kuɗin tun kafin naka ya fito. Idan za ka karɓi naira miliyan 5, za a iya buƙatar ka bada miliyan 2, kafin a fitar  da kuɗin. 

Ta kai munzalin da a hakan ma sai kana da ƙafa za ka samu wannan dama. Domin akwai mutanen da a shirye suke su sadaukar da wannan kaso don kuɗaɗensu su fita, amma shi ma sai da wanda zai tsaya musu. 

Shin mecece makomar irin waɗannan azzaluman ma’aikata da shugabanni da suke cin irin waɗannan kuɗaɗe? Da yawan masu bin waɗannan kuɗaɗe sun rasu ba su ji ko ƙamshin waɗannan haƙƙoƙin nasu ba, amma hakan bai zama izina ga waɗannan shugabannin ba, su yi tunanin  cewa su ma za su je wannan guri. 

Duk irin shahararka da gudunmawa da ka bayar a jiharka ko ƙasarka, daga inda Allah ya ɗauki ranka, babu wanda zai taimaka wajen a biya magada haƙƙoƙininsu. 

Wasu fitattun ma’aikata ne, wasu ma ‘yan jarida ne da suka riƙe muƙamai a ƙungiyoyin ‘yan jarida, amma tun da suka kwanta dama babu wanda zai ce ya dace a biya iyalansu abin da yake haƙƙinsu. Ina ga ƙaramin ma’aikaci da ba kowan kowa ba?

Shi ya sa dole a yaba wa tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau. A lokacin da ya hau kujerar gwamnan Kano, ya ce ko da kuɗaɗen jihar Kano za su ƙare, sai ya biya abin da yake haƙƙi ne na tsofaffin ma’aikata. 

A zamanin Shekarau,  duk wanda suka yi ritaya, ba su sami wannan matsala ba. Wasu ma da gwamnatinsa ta zo ƙarshe, suka fahimci abubuwa za su iya sauyawa sai suka yi ritaya suka karɓi haƙƙoƙinsu duk kafin lokacin barin aikinsu ya yi. 

Wannan hasashe da farar dabarar tasu za ta tabbatar maka da cewa mutanenmu na da baƙin halin da zalunci na ƙin ƙarawa. Ai ko sai hasashen  nasu ya tabbata, na tunanin ba kowanne gwamna ne zai ɗora a kan wannan aikin alheri ba. Kuma hakan ta tabbata a jihar Kano, yanzu hannun agogo ya koma baya. 

Wasu na kawo dalilai na rashin biyan wannan kuɗaɗe, amma duk ba su da tushe bare makama. A wannan lokaci na dimokaraɗiyar da muke ciki, gwamnan jihar Borno Farfesa Umara Babagana Zulum ya sanar da gama biyan duk wani haƙƙi na duk wani tsohon ma’aikaci a jiharsa, duk da ƙalubale da jiharsa ta shiga na rashin tsaro da garawar harkokin kasuwanci yadda ya kamata. Shin sauran jihohi sun fi shi matsaloli da rushewar tattalin arziƙi ne?

Abin takaici ne a ce shugabannin siyasa sun mayar buƙatun al’umarsu koma baya, yadda abin da zuciyarsu take so ko ‘yan kanzaginsu suke so, su ne kaɗai buƙatu. 

Ai rashin hangen nesa ne, a kwashe kuɗaɗen ƙananan hukumomi a zuba su a aikin gina gadojin sama, alhali waɗanda za su hau gadojin na fama da yunwa, wasu ma sun kamu da ciwon shanyewar varin jiki. Ina su ina hawa gada?

Ita fa dimokaraɗiya, buƙatu da walwalar jama’a shi ne ruhinta. Malam Aminu Kano ya kalli siyasa a matsayin yadda za a tafiyar da ɗan’adam. Ashe jigonta ya ta’allaƙa ne da yadda za a gina ɗan’adam ya samu rayuwa ingantacciya. 

Wasu gine-gine da kwaskwarima na biyowa ne bayan an fara gina rayuwar ɗan’adam. Wannan shi zai ba shi saiti tare da ƙoƙarin gina rayuwa ingantacciya.

Shuganninmu bini-bini suna Turai ko sun tafi sabuwar duniyar Dubai, wadda ba a jima da gina ta ba. Sun bar nasu al’ummar cikin baqin talauci da fatara da rashin aiki yi, babu kyakyawan muhalli da asibitoci, babu ingantatcen ilimi. 

Waɗannan ƙasashe da suke sha’awa suke kai ‘ya’yansu karatu ba haka aka wayi gari aka gansu ba. Mutanen ƙasar ne suka yi aiki tuƙuru suka gina su bisa bin dokokin ƙasarsu. 

Amma abin haushi shi ne, duk wannan yawon nasu bai sa sun fahimci yadda za su kwaikwayi tsari cigaba da gina ɗan’adam ba a yawon da suke zuwa. 

A irin waɗannan qasashe na Turai an so a ƙara wa ma’aikata wa’adin ritaya daga aiki, amma suka fito suka yi bore. Savanin tamu ƙasar da ma’aikata ba sa fatan a ce ga ranar ritayarsu ta zo, saboda fargaba da halin rashin jin daɗi da za su shiga. 

Idan har muna so rayuwarmu ta inganta, sannan ƙasarmu ta samu tagomashi, sai mun tashi mun yaƙi wannan rashin adalcin. Babu yadda za a yi akwai haƙƙoƙin wasu bayin Allah a ƙasarmu ko jihohinmu da aka cinye mu ga daidai. 

Duk waɗanda suka jawo waɗannan matsaloli wakilanmu ne. Don haka ba mu da wata hujjar cewa ba mu da rawa a taɓarɓarewar wannan al’amari. Ba don komai ba sai don wakilcin da muka ba su. Mu ne muke da ikon mu ce ga yadda muke so a wakilce mu. Muna da ikon mu ce waje kaza ba haka ya kamata a yi ba, ga yadda ya kamata a yi. 

Malam Kallah marubuci ne na cikin harshen Turanci da ma Hausa, kuma tsohon shugaban Ƙungiyar Marubuta Ta Najeriya (ANA), reshen jihar Kano. Ana iya samunsa ta email: [email protected]