2023: IBB ya yi wa Saraki mubaya’a

Daga BASHIR ISAH

Tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana goyon bayansa ga tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr Bukola Saraki, kan ƙudirinsa na takarar kujerar shugaban Nijeriya don zama magajin Shugaba Buhari ya zuwa 2023.

IBB ya bayyana goyon bayan nasa ga Saraki ne a lokacin da yake amsa buƙatar tawagar kamfen ɗin Saraki sa’ilin da suka ziyarce shi a gidansa da ke Minna, jihar Neja, ƙarƙashin jagorancin shugaban tawagar, Farfesa Hagher Iorwuese da Darakta-Janar ɗinsa, Chief Osaro Onaiwu.

Tawagar yaƙin nema wa Saraki zaɓe ta ziyarci tsohon shugaban ƙasar ne musamman don nema wa Saraki mubaya’arsa kan aniyyarsa ta takarar shugaban ƙasa.

Kai tsaye Babangida ya bayyana goyon bayansa ga Saraki ba tare da wani kauce-kauce ba, yana mai cewa, ‘yan takara da dama sun ziyarce shi, amma a matsayin Saraki na wanda ya yi wa ƙasar farin sani shi ya kamata ya jagoranci ƙasar zuwa ga samun gagarumar cigaba.

A cewarsa, “Na yi farin cikin samun mutanen da suka ayyana wanda ya kamata ya zama shugaban Nijeriya na gaskiya, wannan ita ce fahimtar da aka rasa. Na ji daɗin yadda kuka zaƙulo wanda zai iya aikin. Dole ne labarin ya canza. Na san ɗan takararku sosai, ina tare da shi. Mahaifinsa ya kasance kusa da ni sosai.

“Ku zaɓi ɗan takarar da ya dace. Da sunan SP nake kiransa, a rumbun makamai akwai wata bindiga da ake kira SP saboda ingancinta da kuma cika aiki, yadda Saraki yake kenan.”

IBB tare da tawagar da ta ziyarce shi

Daga nan IBB ya yaba wa Saraki bisa ƙoƙarin da ya yi wa ƙasa a matsayinsa na Shugaban Majalisar Dattawa zubi na takwas, tare da cewa ƙoƙarin nasa ne ya ceci ƙasar nan daga faɗawa wani hali mara daɗi a wancan lokaci.

Sai dai ya ce, tawagar kamfe ɗin sai sun yi aiki sosai don fahimtar da takwarorinsu da ma ‘yan Nijeriya, amma cewa lallai sun zaƙulo ɗan takarar da ya dace da shugabancin Nijeriya.

Tun farko sai’ilin da yake bayani kan dalilin ziyarar tasu, jagoran tafiyar, Farfesa Hagher ya buƙaci IBB da ya sanya wa tafiyarsu albarka sannan ya mara wa Saraki baya don cimma ƙudirinsa a 2023.