Yadda Farfesa Wakawa ya tsere wa tsara wajen kula da rayuwar al’umma

Daga ABDULLAHI GAMBO

Farfesa Ibrahim Abdu Wakawa, ƙwararren likita ne da ya yi shura wajen cigaban rayuwar al’umma, mutum ne mai tsananin kishi da nuna jinƙai ga gajiyayyu da masu ƙaramin ƙarfi; shi ne Babban Darakta (CMD) kuma babban jami’in kula da lafiya a asibitin kula da masu matsalar ƙwaƙwalwa ta tarayyar Nijeriya da ke Maiduguri. 

Wakawa ya yi ilimi mai zurfi a ɓangaren sanin ƙwayoyin cututtuka da kuma ilimin sanin gaɓoɓin ɗan Adam a Maiduguri, cikin shekarar 2001. Sanan ya samu horo na musamman a kan ilimin matsalar ƙwaƙwalwa a Kwalejin Sanin Gaɓoɓin ɗan Adam ta Afirka a shekarar 2009.

Ƙwararren likitan ya samu shaidar kasancewar sa mamba na ƙungiyar ƙwararru a kan rage shan miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya, sannan kuma mamba ne a Kwalejin zurfafa ilimi a kan fannin likitanci ta Nijeriya.

Farfesa Abdul Wakawa ya soma aikinsa a matsayin Daraktan Asibiti (CMD) a shekarar 2016. Daga nan kuma ya ci gaba da taka rawar gani ta hanyar samar da muhimman ayyuka a asibitin a matsayin gudunmuwarsa ga kiwon lafiya a Nijeriya. 

Daga cikin ayyukansa sun haɗa da, samar da ɗakunan gwaje-gwaje da ɗaukar hoton lalurar marasa lafiya a zamanance, zamanantar da hanyar adana bayanan marasa lafiya i zuwa na’ura mai ƙwaƙwalwa, ɗakunan kula da masu taɓin hankali da sassaita masu shaye-shaye, samar da rijiyoyin burtsatse da sauran ayyuka masu yawa.

A shekarar 2019 ma, Wakawa ya samar da ayyuka masu yawa da muhimmanci kamar ɓangaren yara, ginawa tare gyara ɗakunan duba marasa lafiya har guda 12, ginawa da gyara ɗakunan ma’aikatan jinya har guda 12, samar da ɗakin karatu da sauransu. 

A shekarar 2020,  bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya ɗora daga inda ya tsaya, inda ya cigaba da samar da ayyukan amfanarwa ga asibitin, waɗanda suka haɗa da samar da ababen hawa guda huɗu don zirga-zirga a asibitin, sannan gyara rufin wasu sassa na kwalejin da ma wasu tarin ayyuka da ya yi wanda hagunsa ba ta san ya yi ba.

A halin yanzu dai Farfesa Wakawa wanda yake da aure har ma da ‘ya’ya, shi ne mataimakin shugaban Ƙungiyar Hana Amfani da Miyagun Sinadarai (ISSUP) ta Nijeriya bakiɗaya. Sannan ya taɓa riqe muqamin Kungiyar Likitoci ta Nijeriya (NMA) reshen Jihar Borno, sannan ya halarci tarurrukan ƙara wa juna sani a fannin kiwon lafiya da dama.

Wakawa ya wallafa ingantattun littattafai aƙalla guda 50 a ɓangaren kiwon lafiya da sauran vangarorin da ya fi shahara a kai. 

Rayuwar Farfesa Wakawa abar koyi ce ga kowane mutum mai kishi da son cigaban al’ummarsa ta fuskoki mabambanta.