Hare-haren Boko Haram/ISWAP sun yi ajalin jami’an tsaro 11 a Neja

*Sanata Sani Musa ya roƙi agajin Gwamnatin Tarayya

Daga BASHIR ISAH

Sanata mai wakiltar Neja ta Gabas a Majalisar Dattawa, Sanata Mohammed Sani Musa na jam’iyyar APC, ya yi tir da mabambantan hare-haren da mayaƙan Boko Haram/ISWAP suka kai a yankunan ƙaramar hukumar Paikoro da Shiroro tsakanin ranakun Juma’a da Asabar da suka gabata.

Bayanai sun nuna sabbin hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar jami’an tsaro 11 tare da jikkata manoma da dama haɗa da lalata dukiya mai tarin yawa a yankuna da lamarin ya shafa.

Cikin sanarwar da ya fitar ranar Laraba a Abuja, Sanata Sani ya bayyana kashe-kashen da ɓarnata dukiyoyin da mayaƙan suka yi a matsayin abin takaici da taɓa zuciya. Tare da yin kira ga jami’an tsaron jihar da su sake ɗamara wajen yaƙi da ‘yan ta’adda da ta’addancinsu a jihar.

Haka nan, ya jaddada kiransa ga Gwamnatin Tarayya da ta taimaka ta kai ɗauki don kuɓutar da jihar daga halin da ta tsinci kanta.

Kazalika, ya nusar da al’ummar da lamarin ya shafa a Galadiman Kogo da Kuchi a yankunan ƙaramar hukumar Shiroro da Munya da su kasance masu taimaka wa jami’an tsaron da muhimman bayanai don kawo ƙarshen matslar tsaro a yankunansu da ma jihar baki ɗaya.

“Abin da ke faruwa da mu a jihar Neja dangane da matsalar tsaro lamarin ya fi ƙarfinmu, wannan ne ya sa muke kira ga Gwamnatin Tarayya da ta taimaka ta kawo mana ɗaukin gaggawa”, in ji Sanata Musa.

Musa ya buƙaci Babban Sufeton ‘Yan Sanda, IGP Usman Alkali da sauran hukumomin tsaro da su matse ƙaimi wajen bincike don bankaɗo waɗanda suka aikata aika-aikar.