Rashin tabbas na tsari ka iya shafar tattara kuɗaɗen shiga na Kwastom – Ƙwararre

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wani masanin harkar tattali mai suna David Ambi, ya ce rashin tabbas na tsari zai taimaka wajen haifar da tsaiko a samuwar Kasafin 2025 ga Hukumar Kwastom (NCS).

Kwantirola Janar na hukumar, Adewale Adeniyi ya ce a ranar 14 ga watan Junairu ne Gwamnatin Tarayya ta ayyana Naira Tiriliyan 6.58 a matsayin kuɗin shigar da take hari a shekarar 2025.

Saidai, Kwamitin haɗaka na kuɗi na Majalisun Tarayya ya ƙara adadin kuɗin shiga na NCS zuwa Tiriliyan N12 a lokacin kare kasafi.

Mista Ambi a wata hira da kamfanin dillancin labarai (NAN), ya ce sauye-sauye da ake samu akai-akai da suka haɗa da dakatar da shigowa da wasu ababe, rugujewar darajar kuɗi da hauhawar farashi ka iya shafar tsarin kasuwanci da kuma haifar da tsaiko ga tattara kuɗaɗen shiga.

Ya yi kira ga hukumar da ta nemi a samar da tsare-tsaren kasuwanci masu kyau gami da haɗe kai da hukumomin gwamnati don tabbatar da tsare-tsaren sun dace da manufofin tattara kuɗaɗen kwastom.

Ya kuma shawarci a riƙa amfani da yanar gizo wajen tattara kuɗaɗen don tabbatar da gaskiya da adalci da ƙaurace wa jinkiri da kuma rage yawan aiki ga ma’aikata.

Har’ilayau, ya yi kira ga NCS da ta ƙarfafa matakan tsaro akan iyakoki da faɗaɗa ayyukanta da kuma damawa da masu-ruwa-da-tsaki a ɓangaren.

By Babaji