
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamna Dauda Lawal na Zamfara da Dikko Raɗɗa na Katsina sun yi wata ganawar sirri da Ministan Tsaro, Badaru Abubakar da Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu.
An gudanar da zaman ne a ranar Talata, a Ma’aikatar Tsaro da kuma ofishin NSA.
Wata sanarwa da Kakakin gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce an yi ganawar ne don tattauna wasu shawarwari da kwamitin tsaro na haɗaɗɗun ƙungiyoyin Arewa (CNG) suka bayar.
Sanarwar ta kuma ce, a watan Janairu, 2024 ne ƙungiyoyin suka gudanar da wani zama na tattauanawa tsakaninsu ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soji a Nijeriya, Janar AbdulSalami Abubakar.
Kakakin gwamnan ya ce, “Gwamnonin sun tattauna manyan ababen da suka shafi rashin tsaro da faɗaɗa hanyoyin haɗin-gwiwa tsakanin jihohin biyu da Ma’aikatar Tsaro.”
Wannan ganawa da gwamnonin suka yi da jigogin tsaron da kuma wakilan kungiyoyin CNG na daga cikin matakan da gwamnonin ke ɗauka wajen ganin an daƙile matsalolin taɓarɓarewar tsaro a jihohin nasu da ma Arewa-maso-Yamman Nijeriya baki ɗaya.
