Majalisar Wakilai ta gayyaci Wike da Daraktan DSS kan rashin tsaro a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Majalisar Wakilai ta gayyaci Ministan Abuja, Nyesom Wike da Darakta-Janar na Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS), Oluwatosin Ajayi da Kwamishinan ƴan sandan Abuja, Peter Opara da sauran masu-ruwa-da-tsaki kan harkar tsaro don daidaita matsalolin tsaro a Abuja.

Majalisar ta ɗauki matakin ne bayan gabatar da wani ƙudiri na muhimmacin kula da garuruwa da Ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Toro ta Jihar Bauchi, Haruna Dabo ya gabatar a zaman Majalisar na ranar Talata.

Dabo ya gabatar da ƙudirin ne jim-kaɗan bayan garkuwa da kuma kashe mai taimaka masa, Ni’ima Sulaiman da wasu ƴan bindiga suka yi a ranar 17 ga watan Oktoba, 2024 duk cewa an biya Naira miliyan 1 kuɗin fansa.

Ya koka game da yadda ayyukan garkuwa da mutane da fashi ya yi ƙamari a birnin, ya na mai bada misali da masu amfani da motocin taxi da ba su da rijista suna yi wa mutane ƙwace, waɗanda ake kira da ƴan ‘one chance’ a babban birnin.

Ya kuma bayyana yadda ƴan bindigar suka ɗauki marigayiyar a yankin Banex a ranar Alhamis, a lokacin da ta nufi tafiya gidansu da ke gundumar Jahi a Wuse II. Bayan biyan kuɗin fansar ne, sai suka tsinci gawarta a yankin Maitama kusa da gadar Minister’s Hill.

Ɗan Majalisar ya bayyana hakan a matsayin abin takaici game da lamarin tsaro a Abuja wanda ya sanya al’umma suka shiga halin ɗar-ɗar.

Majalisar ta kuma umarci kwamitinta na Abuja ya binciki motocin da ba su da rijista da fenti da ɗaukar matakan gudanar da zirga-zirgarsu.

Bugu da ƙari, kwamitin tare da kwamitocin ƴan sanda da Tsaron Ƙasa, an ɗora musu nauyin bincike game da ayyukan masu garkuwa da mutane da ƴan fashi inda ake tsammanin su fitar da rahotonsu nan da sati uku.

By Babaji