Wasu jami’an rundunar sojan saman Nijeriya sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a kan hanyar Jos zuwa Akwanga.
Haɗarin ya auku a ranar 22 ga watan Oktoba yayin da jami’an ke hanyar zuwa Abuja domin halartar wani taron wasanni inda motar su tayi karo da wata babbar mota da ke tafe.
Daraktan yaɗa labari na rundunar sojan saman, Air Comodore Olusola ya tabbatar da faruwan wannan lamarin, inda ya nuna irin halin baƙin ciki da rundunar ta ke ciki domin waɗannan gagaruman rashi.
Olusola ya cigaba da bayyana yadda rundunar sojan za ta cigaba da tallafawa iyalan mamatan. Ya roƙi jama’a da su mutunta sirri na iyalan.
Daga ƙarshe ya yi addu’ar Allah ya jiƙan su da gafara.
