Daga AISHA ASAS
Masana’antar fina-finan Hausa ta shiga cikin yanayi na jimami da alhini bayan rasuwar tsohuwar jaruma Wasila Isma’il, wadda ta kasance cikin taurarin farko da suka taka muhimmiyar rawa wajen kafa tubalin da masana’antar Kannywood ta tsaya a kai a yau. Rasuwarta ba wai mutuwar jaruma kaɗai ba ce, tamkar rufe wani babi ne na tarihin tsohuwar Kannywood da mutane da dama suka taso suna kallo.
An bayyana cewa, jarumar ta rasu tana da shekaru 46 bayan fama da jinya, lamarin da ya jefa masoyanta da abokan sana’a cikin jimami.
Wacce ce Wasila Isma’il?
An haifi Wasila Isma’il a garin Kaduna, inda ta yi karatun firamare da sakandare kafin daga bisani ta samu diploma daga Kaduna State Polytechnic. Tun kafin ta shiga harkar fim, mutane da dama sun santa da nutsuwa da halin kawaici. Haka kuma ta taso da burin shiga harkar da za ta sa ta bayyana baiwarta ga duniya.
Lokacin da masana’antar Kannywood ke tasowa a ƙarshen shekarun 1990, Wasila na daga cikin matan farko da suka yi ƙwazo da jarumtar shiga harkar fim a lokacin da iyaye da al’umma da dama ke kallon sana’ar da wani irin tsoro da kyama. Wannan ya sa fitowarta a wancan lokaci ta zama wani abin lura musamman ga matan Arewa.
Masu sharhi kan harkar fim sun bayyana cewa, Wasila na daga cikin mata kaɗan da suka taimaka wajen sa mutane suka fara kallon fina-finan Hausa da wani sabon ido, musamman saboda yadda take iya taka rawa cikin natsuwa ba tare da wuce gona da iri ba.
Shigarta harkar fim da yadda sunan “Wasila” ya zama tarihi:
A tarihin Kannywood, akwai fina-finai kaɗan da suka sauya rayuwar jarumi gaba ɗaya kamar yadda fim ɗin Wasila ya sauya rayuwar Wasila Isma’il. Kafin fitowar fim ɗin, tana daga cikin sabbin fuskokin da ke ƙoƙarin samun gurbi a masana’antar da ke tasowa a lokacin. Amma bayan fitowar fim ɗin, sunanta ya shiga cikin jerin jaruman da kusan kowane mai kallon fina-finan Hausa ya sani.
An shirya fim ɗin ne a shekarar 1999 a lokacin da masana’antar Kannywood ke cikin matakin gina kanta. A wancan lokaci, fina-finan Hausa ba su da yalwar kuɗi ko kayan aiki irin na yanzu, amma suna da labarai masu ma’ana da taɓa zuciya da kuma jarumai masu baiwa. Wannan ne ya sa fim ɗin ‘Wasila’ ya samu karɓuwa sosai a tsakanin masu kallo musamman a Arewacin Najeriya.
Fitaccen jarumi Ali Nuhu ne ya fito tare da ita a fim ɗin, yayin da Yakubu Lere ya jagoranci shirinsa. Masu nazarin tarihin Kannywood sun bayyana cewa, fim ɗin na daga cikin ayyukan farko da suka taimaka wajen kafa Ali Nuhu da Wasila a matsayin manyan taurari masu tasowa a lokacin.
Sai dai abin da ya fi jan hankali shi ne, yadda sunan fim ɗin ya zama sunan da ya mamaye rayuwar jarumar gaba ɗaya.
A wata hira da aka sake yaɗawa bayan rasuwarta, Wasila ta bayyana cewa, asalin sunan fim ɗin ‘Jamila’ ne, amma ita kanta ta nemi a sauya sunan saboda tana jin tsoron kada sunan ya haifar mata da matsala ko rashin fahimta daga al’umma. Daga bisani aka sauya shi zuwa ‘Wasila’, kuma wannan suna ne daga baya ya zama alamar da ta rayu da ita har zuwa rasuwarta.
Bayan fitowar fim ɗin, Wasila ta zama ɗaya daga cikin jaruman mata da aka fi nema a masana’antar. Masu shirya fina-finai sun fara ganin cewa tana da wata irin nutsuwa da iya sarrafa motsin rai a fim, musamman a labaran soyayya da na iyali. Wannan ya sa ta samu damar fitowa a wasu fina-finai da dama a farkon shekarun 2000.
Masoya Kannywood na wancan lokaci sun bayyana cewa, fim ɗin ‘Wasila’ ya yi tasiri musamman ga mata masu kallo saboda yadda aka gabatar da halayen cikin natsuwa da tarbiyya. A lokacin, masana’antar na ƙoƙarin tabbatar wa iyaye cewa, fina-finan Hausa ba wai kawai nishaɗi ba ne, har ila yau suna ɗauke da darussa da al’adun Hausawa.
Sai dai shaharar da fim ɗin ya kawo mata ta zo ne tare da wasu ƙalubale. A wancan lokaci, jaruman mata a Kannywood na fuskantar matsin lamba daga al’umma, musamman saboda yadda wasu ke kallon harkar fim a matsayin sana’ar da ba ta dace da mata ba. Wasila na daga cikin waɗanda suka fuskanci irin wannan suka da kallon wariya daga wasu sassa na al’umma.
Rahotanni daga mutanen da suka yi aiki tare da ita sun nuna cewa, duk da irin wannan ƙalubale, ta ci gaba da nuna jajircewa da natsuwa a aikinta. Wannan ne ya sa wasu ke kallonta a matsayin ɗaya daga cikin matan farko da suka taimaka wajen sa iyalai da dama suka fara amincewa da kallon fina-finan Hausa a gidajensu.
Wani babban tasirin fim ɗin ‘Wasila’ shi ne yadda ya taimaka wajen kafa tsarin taurarin mata a Kannywood. Kafin lokacin, yawancin hankalin masana’antar ya fi karkata kan jarumai maza. Amma bayan nasarar fim ɗin, an fara ganin cewa jaruman mata ma na iya ɗaukar nauyin fim tare da jawo hankalin masu kallo.
Har zuwa yau, idan aka ambaci tsofaffin fina-finan Hausa da suka bar tarihi, fim ɗin ‘Wasila’ na cikin ayyukan da masu kallon Kannywood ke tunawa da su saboda rawar da ya taka wajen haɓaka masana’antar da kuma sauya rayuwar jarumar da ta ɗauki sunansa har zuwa ƙarshen rayuwarta.
Rayuwar aurenta da zaman gida:
Bayan shahara a harkar fim, Wasila ta shiga rayuwar aure da Al-Amin Chiroma. Tsawon shekaru ana kallon aurensu a matsayin ɗaya daga cikin auren da suka daɗe suna tafiya lafiya a cikin masana’antar Kannywood, musamman a lokacin da aurarrakin jarumai da dama ke rushewa cikin ƙanƙanin lokaci.
Rahotanni sun nuna cewa, aurensu ya ɗauki kusan shekaru 20, kuma Allah Ya albarkace su da ‘ya’ya huɗu — mata uku da namiji ɗaya.
A tsawon lokacin aurensu, Wasila ta rage bayyana a harkokin Kannywood, lamarin da wasu ke dangantawa da mayar da hankali kan rayuwar iyali da tarbiyyar yara. Duk da haka, ba ta fice gaba ɗaya daga harkar kafafen yaɗa labarai ba, domin ta yi aiki a Liberty Radio Kaduna a matsayin mai shirye-shiryen rediyo.
Rabuwar aurenta da abin da ya biyo baya:
Duk da tsawon shekarun zaman aurensu, daga bisani labari ya bazu cewa, Wasila da mijinta sun rabu. Rahotanni daga wasu kafafen Hausa sun nuna cewa, rabuwar tasu ta girgiza mutane da dama a Kannywood saboda yadda aka daɗe ana kallonsu a matsayin ma’aurata masu jure wa ƙalubale.
Mutane da yawa sun bayyana mamaki musamman ganin yadda aurensu ya daɗe kafin rabuwar ta zo. A lokacin, an yi ta ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke nuna damuwa kan yadda tsofaffin jarumai ke fuskantar sauye-sauyen rayuwa bayan shahara ta ragu.
Bayan rabuwar aurenta, Wasila ta ƙara nesanta kanta daga hasken fina-finai da yawan bayyana a bainar jama’a. Wasu na kusa da masana’antar sun bayyana cewa, ta fi mayar da hankali kan iyalinta da kuma kula da lafiyarta.
Sai dai duk da rashin yawan fitowarta a fina-finai a shekarun baya-bayan nan, tsofaffin masoya Kannywood ba su taɓa mantawa da ita ba. Duk lokacin da aka ambaci tsofaffin jaruman da suka kafa tarihin masana’antar, sunanta na cikin waɗanda ake fara kawowa. Sannan ‘yan fina-finan da ta samu fitowa waɗanda ba su da yawa sun samu karɓuwa daidai gwargwado, wanda hakan ba zai rasa nasaba da masoyanta da suka yi kewar ta ba.
Rasuwarta ta girgiza Kannywood:
A ranar Lahadi, 24 ga watan Mayun 2026 ne aka tabbatar da rasuwar Wasila Isma’il bayan fama da rashin lafiya. Ta rasu ne a asibitin FOMWAN da ke Kaduna.
Tsohon mijinta, Al-Amin Chiroma, shi ne ya fara tabbatar da rasuwar tata ta hanyar sanarwa a kafafen sada zumunta, inda ya bayyana jimaminsa tare da addu’ar Allah Ya jikanta.
Nan take bayan labarin ya bazu, shafukan sada zumunta suka cika da saƙonnin ta’aziyya daga jarumai, masu shirya fina-finai da masoya daga sassa daban-daban na Arewa.
Fitaccen jarumi Ali Nuhu wanda suka yi suna tare a fim ɗin Wasila, ya bayyana alhininsa tare da yi mata addu’ar Allah Ya gafarta mata kuma Ya sa Aljanna ce makomarta.
Rawar da ta taka a Kannywood da ra’ayin jama’a:
Mutane da dama na kallon Wasila Isma’il a matsayin ɗaya daga cikin matan da suka taimaka wajen kafa martabar jaruman mata a farkon Kannywood. A lokacin da masana’antar ke cike da ƙalubale da suka haɗa da suka daga al’umma, Wasila ta kasance cikin waɗanda suka tsaya suka nuna cewa ana iya yin fim cikin mutunci da da kiyaye martaba.
Masoya fina-finan Hausa sun bayyana cewa, rawar da ta taka ba wai kawai ta tsaya kan fim ɗin ‘Wasila’ ba, ta kasance ɗaya daga cikin fuskokin da suka taimaka wajen jawo hankalin mata da iyalai zuwa kallon fina-finan Hausa a farkon shekarun Kannywood.
Wasu daga cikin tsofaffin masu kallon Kannywood sun bayyana cewa, mutuwarta ta tuna musu da zamanin da masana’antar ke cike da labarai masu tarbiyya da salo irin na gargajiyar Hausawa.
A yau, duk da cewa sabbin jarumai sun mamaye masana’antar, sunan Wasila Isma’il na ci gaba da kasancewa cikin tarihin jaruman farko da suka kafa tubalin Kannywood da sadaukarwa, juriyya da kuma baiwar fasaha.
