
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ofishin Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (ONSA) ya yi watsi da ikirarin shigowa da sinadarin guba na ‘thallium sulphate’ daga ƙasar Poland.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya bayyana al’amarin ta kafar X cewa, ‘yan ɓangaren adawa sun samu labarin da ke cewa hukumar ta shigo da kimamin kilograms 10 na sinadarin cikin Nijeriya.
Ya ce, ya aike wa Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro, Nuhu Ribaɗu wasiƙar neman ya fayyace bayani akan al’amarin da ake tuhumar ofishin nasa a kai.
A cikin wasiƙar, El-Rufa’i ya bayyana sinadarin a matsayin guba mai haɗarin gaske da ba ta da launi ko wari, yana mai nuna damuwarsa akan hatsarinsa ga tsaron al’umma gami da kira da a fito da bayaninsa a fili.
Haka kuma, ya nemi a yi bayanin dalilin da ya sa aka kawo sinadarin Nijeriya, waye ya yi amfani da shi, daga wane kamfani aka sayo shi, sannan ko da sahalewar hukumomin Nijeriya a hukumance da dai sauransu.
Saidai, a wata hira da jaridar Vanguard, wani babban jami’in ONSA ya yi watsi da ikirarin, inda ya bayyana shi a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama’a.
Ya bayyana cewa, hukumar ba ta sayi wani sinadarin guba ba kamar yadda aka yi ikirarin.
El-Rufa’i, wanda a ‘yan kwanakin nan ya shahara da sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ‘yan ɓangaren adawa, zai hallara a gaban Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa, EFCC.
