Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin wucin gadi na hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) amincewa da tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark a matsayin shugaban riƙo na ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam’iyyar ADC.
An ruwaito cewa Mai Shari’a Emeka Nwite, wanda ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, ya bayar da umarnin wucin gadi ne biyo bayan wani ƙudiri da Nafiu Gombe ya gabatar a ranar 2 ga Satumba, 2025, wanda ke ƙalubalantar sahihancin naɗin mutanen biyu.
ƙudirin ya lissafo: ADC a matsayin wanda ake ƙara na ɗaya, David Mark a matsayin mai ƙara na biyu, Rauf Aregbesola a matsayin wanda ake ƙara na 3, INEC a matsayin wadda ake aara na huɗu da Ralph Nwosu, tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, a matsayin wanda ake ƙara na 5.
Mai shigar da ƙarar na neman dakatar da abin da ya bayyana a matsayin kwace shugabancin jam’iyyar ba bisa ƙa’ida ba har sai an saurari wata kwakkwarar hujja.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Nwite ya haramtawa INEC musamman daga: amincewa da Mark da Aregbesola a matsayin shugabannin riƙon kwarya na jam’iyyar ADC ta ƙasa, da kuma amincewa da wakilansu ko yin aiki a madadinsu a kowane mukami da kuma nuna sunayensu a shafin yanar gizon hukumar ko kuma bayanan hukumar INEC a matsayin shugabannin riƙo na jam’iyyar.
“An ba da umarnin umarnin wucin gadi na hana wanda ake ƙara na 4, INEC, daga amincewa da waɗanda ake kara na 2 da na 3 ko kuma wakilansu a matsayin shugaban riƙo na ƙasa kuma sakataren jam’iyyar ADC na ƙasa, har sai an saurari ƙarar da kuma yanke hukuncin kan ƙarar,” inji mai shari’a Nwite.
Kafin yanke hukuncin, INEC ta riga ta sabunta shafinta na yanar gizo inda ta sanya Mark da Aregbesola a matsayin shugaban riƙo da sakatare na ADC, lamarin da ya haifar da cece-kuce a cikin jam’iyyar.
Jam’iyyar ADC dai ta sha fama da rigingimun cikin gida tun ƙarshen wa’adin da Ralph Nwosu ya yi a matsayin shugaba. Nwosu, wanda ya jagoranci jam’iyyar kusan shekaru ashirin, ya fuskanci adawa daga ɓangarori masu kira da a sake sabon shugabanci.
Ana dai kallon naɗin Mark da Aregbesola a matsayin wani yunƙuri na daidaita jam’iyyar gabanin zaɓukan 2027, sai dai wasu masu ruwa da tsaki sun yi kakkausar suka ga matakin da suka ɗauka na cewa ba a bi ƙa’ida ba wajen miƙa mulki.
Kotun ta tsayar da ranar da za a saurari ƙarar a kan sanarwar, wanda zai tabbatar da ko za a ci gaba da dawwama kan ko za a ci gaba da zama na wucin gadi.
