Kotu ta yanke wa kwamandan Ansaru hukunci ɗaurin shekaru 15

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata Babbar Kotu a Abuja ta yanke wa Mahmud Muhammad Usman (Abu Bara’a), ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan kaso.

Abu Bara’a, wanda Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta gurfanar ranar Alhamis, ya amsa laifin gudanar da harkokin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ya ba shi damar mallakar makamai da aikata ayyukan ta’addanci da kuma yin garkuwa da mutane.

Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya bayar da umarnin a ajiye Mahmud Usman a ofishin Hukumar DSS har zuwa lokacin da za a kammala shari’a kan sauran zarge-zargen da ake yi ma sa guda 31.

A lokacin gabatar da ƙarar, an tuhumi Mahmud Usman da Abubakar Abba da aikata ta’addanci a 2022, ta hanyar kai hari kan barikin soji ta Wawa da ke Ka’inji a ƙaramar hukumar Borgu ta Jihar Neja, lamarin da ya yi sanadiyar kisan mutane da dama.

Ana zargin su da koyon horo a kan sarrafa makamai da haɗa bama-bamai a sansanonin ’yan ta’ada da dama.

Mai Shari’a Nwite ya sanya ranar 21 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a ci gaba da shari’ar.

An ruwaito yadda aka gurfanar da mutanen biyu, Mahmud Muhammad Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a, da mataimakinsa Abubakar Abba, wanda aka fi sani da Mahmud Al-Nigeri ko Mallam Mamuda kan tuhume-tuhume 32 da suka shafi ta’addanci.

Tuhuma ta farko ta ce, mutanen sun taimaka wajen tsarawa da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru tsakanin 2013 zuwa 2015, ƙungiyar mai alaƙa da Al-ƙaeda wadda gwamnatin Nijeriya ta haramta.

Abu Bara’a dai ɗan asalin ƙaramar Hukumar Okene ne ta Jihar Kogi, yayin da Mahmud Al-Nigeri ya fito daga ƙaramar Hukumar Daura ta Jihar Katsina.

An kama su ne yayin wani samame da hukumomin tsaro da na leƙen asiri suka gudanar tsakanin watan Mayu zuwa Yulin 2025.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ne, ya bayyana kama su a ranar 16 ga watan Agusta, a Abuja.

By ukarofi