Gwamnatin Tarayya ta karɓi harajin biliyan N600 daga Facebook, Netflix da sauransu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta samu nasarar karɓo harajin da ya kai sama da Naira biliyan 600 na harajin VAT daga kamfanonin da ke samar da sabis na zamani na ƙasa da ƙasa irin su Facebook, Amazon, da Netflix, lamarin da ke nuna wani ci gaba a harkar harajin da Nijeriya ke faɗaɗawa.

Manhaja ta ruwaito cewa, Mista Mathew Osanekwu, mai bai wa shugaban kwamitin shugaban ƙasa shawara kan harkokin haraji ne ya bayyana hakan a yayin wani taron ƙarawa juna sani da manema labarai a Abuja ranar Laraba.

A cewar Osanekwu, gyaran da aka yi wa dokar harajin VAT a yanzu ya bai wa hukumar tara haraji ta tarayya (FIRS) damar baiwa kamfanonin da ba na mazauna gida ba da ke ba da hidima a Nijeriya su biya.

“Waɗannan ba kamfanonin Nijeriya ba ne, amma yanzu suna biyan ɓAT a ƙarƙashin sashe na 10 na dokar ɓAT. An yi rajista a Nijeriya kuma an naɗa su a matsayin wakilan tattarawa,” inji Osanekwu, yana mai jaddada cewa matakin ya yi daidai da mafi kyawun ayyuka na duniya kuma yana tabbatar da cewa Nijeriya ta ci gajiyar haraji kan ayyukan da ake cinyewa a cikin gida amma kamfanonin waje ke bayarwa.

Shi ma da yake jawabi ga mahalarta taron, shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan manufofin kasafin kuɗi da sake fasalin haraji, Farfesa Taiwo Oyedele, ya ƙaryata raɗe-raɗin cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓullo da sabbin haraji.

“Ba sabon haraji ba ne, wasu na ganin shugaban ƙasar ya ɓullo da haraji bayan haraji, kuma ina ƙalubalantarsu da su nuna wani sabon harajin da aka gabatar,” inji Oyedele.

Ya tunatar da ’yan Nijeriya cewa a watan Yulin 2023, watanni biyu da cika wa’adin mulkinsa, Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan wasu umarni guda hudu na dakatar da harajin da aka sanya a kwanakin ƙarshe na gwamnatin da ta gabata, ciki har da harajin fitar da kayayyaki na robobi da shigo da motoci.

“Da yawa daga cikinmu ba ma sane ba saboda shugaban ƙasar bai yarda waɗannan harajin su yi aiki ba, an dakatar da su kuma daga ƙarshe an cire su,” inji Oyedele.

Ya kuma yi ƙarin haske da cewa, harajin da ake ta cece-kuce akan harkar tsaro ta Intanet, tsohuwar doka ce, ba wai gwamnatin Tinubu ce ta ƙirƙiro ba.

Sake fasalin kasafin kuɗi da haraji, wanda ake sa ran zai fara aiki a watan Janairun 2026, an tsara shi ne don yin garambawul ga tsarin harajin Nijeriya mai rauni, faɗaɗa samar kuɗaɗen shiga, da kuma inganta bin doka.

Adadin harajin da Nijeriya ke samu a halin yanzu ya kai kashi 10.8 cikin 100, wanda ya yi ƙasa da matsakaicin kashi 16 cikin 100 na Afirka da kuma ma’aunin duniya na kashi 30 cikin 100.

By ukarofi