
Daga BELLO A. BABAJI
An shiga tashin hankali a yayin da rikicin fili ya haddasa tashin-tashina a tsakanin ƙabilun Hausawa da na Gwarawa a ƙauyen Chimbi dake Ƙaramar Hukumar Paikoro a Jihar Neja.
Sahara Reporters ta ruwaito ta wata ɗaukar bidiyo da hotuna yadda aka cinna wuta a wani yanki na ƙauyen da kuma jiyo ƙarar bindiga a bayan fage.
Zuwa Lahadi da rana ba a iya tantance waɗanda suka samu raunuka ko rasa rai ba, saidai an gano cewa rikicin ya ɓarke ne akan batun fili.
Al’ummar Gbagyi da ake kira da Gwarawa a hausance a Neja, suna da tarihin rikici akan mallakar filaye da kula da su musamman da takwarorinsu na Fulani, wanda a lokuta da dama kan haifar da tashin-tashina kan filayen noma da na kiwo.
A watan Yulin 2016, an samu rikici tsakanin ɓangarorin biyu da ya haddasa mutuwar mutane huɗu da ɗaiɗaita wasu 250 bisa rashin jituwa akan fili da yin kiwo a Ƙaramar Hukumar Bosso.
Haka ma a Agustan 2024, inda aka samu rikici a gundumar Beji ta ƙaramar hukumar bayan zargin wasu makiyaya da kisan wani manomi, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane da dama da raunata wasu, yayin da wasu suka ƙaurace wa gidajensu.
Daga nan ne ƙungiyar Miyetti-Allah ta umarci mambobinta da su janye gudanar da harkokinsu a wata babbar kasuwa dake jihar, wanda hakan ya yi babban tasiri ga harkokin tattali.
