Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙara ta da ƙayar baya kan Greenland, wani yanki mai muhimmanci a tsaron Arctic da ke ƙarƙashin ikon Denmark.
Rahotanni sun nuna cewa Amurka na so ta ƙara samun iko a yankin, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a Turai. ƙasashen Turai sun bayyana damuwa kan wannan mataki, inda Faransa ta nemi atisayen NATO a Greenland domin tabbatar da tsaro da haɗin kai a yankin Arctic.
Shugaba Emmanuel Macron ya ce: “Turai ba za ta janye ko ta amince da tilastawa ba; haɗin kai da mutunta dokokin ƙasa da ƙasa su ne ginshiƙin tsaron duniya.”
