Rikicin PDP ya caɓe yayin da tsagi ya dakatar da Damagum da naɗa sabon shugaban jam’iyya

Spread the love

Rikicin babbar jam’iyyar adawa (PDP) ya ƙara ƙamari yayin da wani sabon ɓangare daga cikin Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya sanar da dakatar da Shugaban jam’iyyar, Umar Damagum da wasu manyan jami’an jam’iyyar guda biyar.

Wanna tsagin ya yi sanarwar ne a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ƙarƙashin jagorancin Sanata Samuel Anyanwu, wanda shi ne sakataren jam’iyyar na ƙasa.

A cewar Anyanwu, an naɗa Mohammed Abdulrahman, mataimakin shugaban jam’iyya na yankin Arewa ta Tsakiya, a matsayin sabon muƙaddashin shugaban PDP.

Ya ce, Damagum da wasu jami’an jam’iyyar sun yi sakacin aiki, cin hanci da saba wa hukuncin kotu, kuma an dakatar da su na tsawon wata ɗaya domin su gurfana gaban kwamitin ladabtarwa.

Sauran waɗanda aka dakatar sun haɗa da Debo Ologunagba, mai magana da yawun jam’iyya; Taofeek Arapaja, mataimakin shugaban jam’iyya (Kudu); Daniel Woyenguikoro, ma’ajin kuɗi na ƙasa; Sulaiman Kadade, shugaban matasan jam’iyya; da Setonji Koshoedo, mataimakin sakataren jam’iyya.

Ya bayyana cewa, za a gurfanar da su gaba ɗaya domin su bayyana dalilin da ya sa ba za a kori su daga jam’iyyar ba.

Saidai a farkon ranar Asabar, tsagin Damagum shi ya fara sanar da dakatar da Sanata Anyanwu da wasu uku daga cikin shugabannin jam’iyyar, lamarin da ke nuna cewa jam’iyyar PDP ta rabu gida biyu a matakin shugabanci na ƙasa.

By Babaji