‘Yan bindiga sun halaka mutane uku da ƙone gidaje a ƙauyukan iyakar Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Al’umma a ƙauyuka da dama sun shiga firgici a Ƙananan Hukumomin Shanono da Tsayawa da ke Jihar Kano biyo bayan wani harin ƴan bindiga da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku da yin garkuwa da mutane.

Al’amarin ya uku ne a daren ranar Juma’a wayewar Asabar, wanda ya jefa al’umma cikin fargaba game da ayyukan ƴan bindiga a ƙauyukan da ke iyakokin jihohin Katsina da Kano.

Wani shaida ya bayyana wa manema labarai cewa kimanin ƴan bindiga guda 20 ɗauke muggan makamai ne suka shiga Ƙauyen Yanganau da ke Tsanyawa, kana daga bisani suka garzaya wasu yankunam Shanono, inda a nan suka halaka mutanen yayin arangama da jami’an haɗaka na ‘jonit security task force’.

Wani mazaunin ɗaya daga cikin yankunan da ya nemi a sakaye sunansa, ya ce maharan sun shigo ne daga Ƙauyen Kogari a Katsina, inda suka farmaki wasu ƴan ƙauyuka, lamarin da ya tilasta wa mutane tserewa daga gidajensu.

Da yake ganawa da manema labarai, wani jagoran al’umma kuma malamin jami’a mai suna Farfesa Muhammad Dauda daga Ƙauyen Kuraku na Gundumar Faruruwa, ya ce al’amarin rashin tsaro ya yi ƙamari duk da cewa akwai jami’an sojoji da na wasu hukumomin tsaron al’umma a yankunan.

Farfesan ya zayyano wasu yankuna da al’amarin ya fi shafar su waɗanda suka haɗa da Goron Dutse, Makama, da Tsaure.

Ya ƙara da cewa hare-haren sun faru ne a Unguwar Tsamiya, Yaudari, da Ƴan Ganau, lamarin da ya ɗaiɗaita al’umma daga muhallansu.

By Babaji