
Daga BELLO A. BABAJI
Tsagin adawa dake jagorantar Majalisar ƙasar Koriya ta Kudu ya amince da tsige Shugaban ƙasar na riƙon ƙwarya, Han Duck-soo.
Majalisar ta tabbatar da hakan ne a lokacin da aka samu ƴanƴanta 190 da suka amince da tsige shugaban a ranar Juma’a.
Han, wanda shi ne Mataimakin shugaban ƙasar, an naɗa shi ne bayan tsige Shugaba Yoon Suk Yeol bisa sauya tsarin mulkin ƙasar a wannan watan wanda majalisar ke ganin hakan ya saɓa wa doka.
Tsige shugaban na riƙon ƙwarya ya ƙara caɓar da siyasar ƙasar tare da yin dameji ga kimarta a idon duniya.
