Ka kiyayi tunzura gwamnatin Nijeriya – Idris ya ja hankalin Tchiani

Spread the love

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

An ja hankalin shugaban gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar, Birgediya Janar Abdourahamane Tchiani, akan ya kiyayi yin kalaman da za su tunzura Gwamnatin Tarayyar Nijeriya.

Kiran ya fito ne daga bakin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar Da Kai na Tarayyar Nijeriya, Alhaji Mohammed Idris, a zantawarsa da BBC Hausa a Abuja, Babban Birnin ƙasar.

Wannan ya biyo bayan zargin da Shugaba Tchiani ya yi a ranar Alhamis, inda ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Nijeriya da ƙoƙarin kawo sojojin Faransa a Nijeriya, don yi wa Jamhuriyar Nijar ƙafar ungulu.

Idris ya ce, “To abin nan ya ba wa gwamnatin Nijeriya mamaki a wani ɓangare, a wani ɓangaren kuma ba mu ji mamaki ba, saboda ai idan ka lura shi Shugaba Tchiani tun da ya hau karagar mulkin nan, yau ya fito da wannan gobe ya fito da wancan. Ana ta kame-kame.”

“Amma mu na bada shawara, ya tsaya ya ƙara nazari a irin wannan maganganu da ya ke, yana ƙoƙarin ya tunzura Nijeriya, mu muna ganin ba daidai ba ne.

“Mu muna da zaɓaɓɓun shuwagabanni, bai kamata shugaban mulkin soja da ya ƙwaci mulki da ƙarfin tuwo ya dawo kuma yana irin wannan bayanai akan gwamnatin Nijeriya ba.”

“Mu muna ganin bai dace ba, ya kamata ya daina yin haka ɗin”, inji Idris.

Minista Idris ya kuma tunatar da Janar Tchiani cewa, a tarihin Nijeriya tun da ta karɓi ƴancin kai ba ta taɓa jibge sojojin ƙasashen waje a cikin ƙasarta ba.

Idan za a iya tunawa, Jamhuriyar Nijar ta jibge sojojin ƙasashen waje da dama a ƙasarta tun bayan samun ƴancin kanta daga Ƙasar Faransa a 1959, amma bayan zuwan gwamnatin soja a ƙarƙashin jagorancin Janar Tchiani a 2023 ta kore su daga cikin ƙasar.

By Babaji