Rikicin siyasar Ribas: Fubara ya sake aike wa ƴan majalisar ɓangaren Wike saƙon gabatar da kasafi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara, ya sake aika saƙo ga Majalisar Dokokin jihar, inda ya ke sanar da ƴaƴanta batun ƙudirinsa na sake gabatar masu da kasafin 2025 don tantancewa da tabbatarwa.

A saƙon, wanda ke ɗauke da ranar 13 ga watan Maris, gwamnan ya sanar da Kakakin Majalisar, Martin Amaewhule cewa ya zaɓi Laraba, 19 ga watan Maris, 2025 a matsayin ranar da zai sake gabatar da kasafin, wanda ya haifar da cecekuce a baya.

Ya ce, ƴan majalisar za su iya zaɓar wata rana da ta fi dacewa da maslaharsu matuƙar wadda ya zaɓa ba ta yi masu ba.

Ya kuma ce, zai cigaba da kiyaye ƙa’idodin doka da hukuncin shari’a domin ciyar da jihar gaba da kuma inganta al’ummarta, ya na mai cewa hakan zai taimaka wajen kawo ƙarshen tataɓurzar da ke hana ruwa gudu a jihar.

Ya ƙara da cewa, duk da bambance-bambancen ra’ayoyin siyasa, maslahar al’umma da ta jihar su ke kan gaba.

A kwanakin kaɗan da suka gabata ne aka hana Gwamna Fubara shiga zauren Majalisar Dokokin, a lokacin da ya je sake gabatar da kasafin.

By Babaji