
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Labarai da Wayar da kan Al’umma, Mohammed Idris, ya tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya na jagorantar al’amura ne a Nijeriya bisa tsananin tsoron Allah da kuma la’akari da irin kyawawan manufofinsa da tarihi zai haska wa duniya a nan gaba.
Ministan ya faɗi hakan ne a yayin taron ganawa da manema labarai na ministoci a ranar Alhamis, inda ya ce ƙasa na samun nasara ne idan jagororinta sun riƙe ragamar shugabanci bisa tsoron ubangijinsu.
Ya ce, gyare-gyare da Shugaba Tinubu ya aiwatar, ba iya bisa kyawawan manufofinsa suka tsaya ba, abubuwa ne da ke da matuƙar muhimmanci ga gina ƙasa da ci-gabanta.
Ya kuma ce, a yanzu al’umma sun fara samun sauƙin hauhawar farashin kayayyakin abinci da ɗorewa ga darajar kuɗin ƙasa, da kuma ragi a farashin albarkatun makamashi, waɗanda ke nuna nasarori da ake samu a ƙarƙarshin gyare-gyaren Shugaban ƙasar.
Ya ƙara da cewa, tarihi ya nuna cewa sauye-sauye masu ma’ana da kyawawan tasiri ga al’umma ba abun ne mai sauƙi ba, ya na mai cewa akwai buƙatar a samu sadaukarwa da jajircewa don samun nasarar da za ta ɗauki tsawon lokaci ana cin moriyarta.
Har’ilayau, Ministan ya ce lallai matakan da gwamnatin Shugaba Tinubu take ɗauka masu tsauri wajen aiwatar da gyare-gyare suna da muhimmanci, ya na mai cewa hakan shi ne fandisho na samar wa ƙasar ci-gaba.
Minista Idris, ya kuma jinjina wa ƴan Nijeriya kan haƙuri da juriyarsu ga hange da tsarin Shugaba Tinubu a yayin jagorantar su.
Kazalika, ya yi kira ga malaman addini da su yi amfani da damar wannan wata na Ramadana wajen yi wa ƙasar addu’ar samun zaman lafiya da tsaro da kuma nasara mai ɗorewa.