Rikita-rikita: Remi Tinubu ta sanya sunan Marigayi Buhari cikin waɗanda suka tallafa mata tara biliyan N20

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Al’umma sun fara cecekuce a yayin da matar Shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta sanya sunan marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari acikin jaddawalin waɗanda suka tallafa mata wajen tara biliyan N20 domin kammala gina ɗakin karatu na ƙasa a Abuja.

A ranar 1 ga watan Satumba matar shugaban ƙasar ta shelanta sadaukar da bikin cikar ta shekaru 65 wanda da za a yi a ranar 21 ga watan, ga kammala gina ɗakin karatu na ƙasa da aka ɗauki tsawon lokaci da farawa.

Akan haka ne ta roƙi abokai, masoya da ɗaukacin al’ummar Nijeriya da su tallafa mata da kuɗi a ƙarƙashin gidauniyarta ta ilimi, wato ‘Oluremi at 65 Education’ domin ƙarasa aikin a madadin saƙonnin taya murna ko kyautuka.

Saidai, hakan ya janyo bayyana mabambanta ra’ayoyi daga manyan ƙasa da sauran al’umma, inda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi ya ce ba daidai ba ne ace ƙasa kamar Nijeriya ta dogara da kuɗin tallafi na zagayowar ranar haihuwa wajen kammala babban aikin ƙasa.

A shekarar 1981 aka ƙaddamar da aikin gina ɗakin karatun ƙarƙashin mulkin Marigayi Shehu Shagari, inda kuɗin kwangilar aikin ya yi ta ƙaruwa daga N8.2bn a shekarar 1981 zuwa N23bn a 2023.

A lokacin da take ganawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa a ranar Talata, Oluremi ta ce al’umma sun tara mata jimillar N20,456,188,924.

Ta kuma yi godiya ga sanannun mutane da dama da suka bada gudumawa ciki har da Shugaba Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da matarsa, tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari, da tsofaffin mata shugabannin ƙasa da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da matarsa, Kakakin Majalisar Wakilai Abbas Tajudeen da matarsa, mambobin Majalisar Dokoki ta Ƙasa, Gwamnoni da matansu da dai sauransu.

Haka kuma, akwai hamshaƙan ƴan kasuwa kamar su Aliko Ɗangote, Abdulsamad Rabi’u, Arthur Eze, Tony Elumelu, Jim Ovia da sauransu.

Saidai sanya sunan marigayi Buhari acikin jaddawalin ya janyo cecekuce da rikitarwa musamman a fagen siyasa da kafafen sada zumunta duba da yadda jama’a da dama ke ƙalubalantar haka.

By Babaji